Atiku Ya Ƙara Gamuwa da Cikas, Sanata Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP, Ya Faɗi Muhimmin Dalili

Atiku Ya Ƙara Gamuwa da Cikas, Sanata Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP, Ya Faɗi Muhimmin Dalili

  • Tsohon hadimin Atiku Abubakar ya kara rikita jam'iyyar PDP yayin da ake tunkarar zaɓen gwamna a jihar Ondo
  • Sanata Kunlere, wanda ya wakilci Ondo ta kudu daga 2011 zuwa 2015, ya fice daga jam'iyyar PDP
  • A wata wasiƙa da ya aike wa shugaban PDP na gundumarsa, ya ce har yanzu bai yanke shawarar jam'iyyar da zai koma ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Sanata Boluwaji Kunlere, wanda ya wakilci mazabar jihar Ondo ta Kudu a majalisar dattawa daga 2011 zuwa 2015, ya fice daga jam’iyyar PDP.

Tsohon sanatan ya fice daga babbar jam'iyyar adawar duk da kasancewar a inuwar PDP ne ya samu nasarar zuwa majalisar dattawa a zaben 2011.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar PDP yayin da aka maka shugabanni a gaban kotun kan abu 1 tak

Sanatan Ondo ya bar PDP.
Sanatan Jihar Ondo, Kunlere, Ya Sauya Sheƙa Daga Jam'iyyar PDP Hoto: Senator Boluwaji Kunlere
Asali: Facebook

Mista Kunlere ya tabbatar da ɗaukar wannan matakin ne a wata takardar murabus da ya aike wa shugaban PDP na gundumar Igbotako 2, ƙaramar hukumar Okitipupa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasiƙar ficewar sanatan daga PDP ta shiga hannun manema labarai a Okitipupa, jihar Ondo yau Alhamis, 25 ga watan Janairu, 2024, kamar yadda Tribune ta rahoto.

A wasiƙar, Sanata Kunlere ya ce:

"A nan ne nake mika takardar ficewa daga jam’iyyar PDP daga ranar 24 ga watan Janairu, 2025. Ina mika godiyata gare ku da sauran ’ya’yan PDP bisa hadin kai da goyon bayan da kuka ba ni a tsawon lokacin da na shafe jam’iyyar.
"Nagode matuƙa Allah ya yi albarka. Haka nan kuma ba zance komai ba, zan yanke shawarar wa zan marawa baya bayan kammala zaɓukan fidda gwani idan Allah ya so."

Kara karanta wannan

Za a yi jana'izar gwamnan APC da ya rasu a kan Mulki, sanarwa ta fito

Wace jam'iyya sanatan zai koma a yanzu?

Dangane da jam'iyyar siyasar da zai koma kuma, Sanata Kunlere ya ce har yanzun bai shiga tattaunawa da kowane jam'iyya ba, kuma bai yanke wacce zai shiga ba.

"A yanzu, ba bu wata jam’iyyar siyasa siyasa da na fara tattunawa da ita," in ji shi.

Kunlere, shi ne daraktan yaƙin neman zaben Atiku Abubakar/Okowa na jihar Ondo a zaben shugaban ƙasar da aka yi a watan Fabrairu, 2023, Daily Post ta rahoto.

Majalisa zata tantance sabon matakin gwamna

A wani rahoton na daban Majalisar dokokin jihar Ondo ta sanya ranar tantance wanda Gwamna Aiyedatiwa ya naɗa a matsayin mataimakinsa.

Kakakin majalisar, Olamide Oladiji, ya ce zasu tantance sabon mataimakin gwamnan ranar Alhamis mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262