Gwamnan APC Ya Nada Sabon Mataimakin Gwamna a Jiharsa
- A karshe, gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya bayyana wanda yake so ya zama mataimakinsa
- Aiyedatiwa ya nada Cif Olayide Owolabi Adelami, a matsayin mataimakin gwamnan jihar Ondo a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu
- Sabon mataimakin gwamnan ya kasance magatakardar majalisar tarayya mai ritaya kuma ya yi takarar gwamnan jihar a 2020 amma ya janyewa marigayi Akeredolu
- Hakan na zuwa ne kasa da awanni shida bayan gwamnan ya rushe mambobin zauren majalisar da magabacinsa, marigayi Rotimi Akerolu ya nada
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Lucky Orimisan Aiyedatiwa, ya bayyana wanda yake so ya zama mataimakinsa.
Aiyedatiwa ya nada tsohon mataimakin magatakardar majalisar dokokin tarayya, Cif Olayide Owolabi Adelami, a matsayin mataimakin gwamnan jihar Ondo, jaridar Leadership ta rahoto.
Nadin Adelami na zuwa ne kimanin awanni shida bayan gwamnan jihar ya tsige yan majalisar zartarwa na jihar a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewat sanarwa daga babban sakataren labaran gwamnan, Mista Ebenezer Adeniyan, an mika sunan sabon mataimakin gwamnan zuwa zauren majalisar dokokin jihar don amincewa da shi, rahoton Punch.
Sanarwar ta ce:
"Majalisar dokokin za ta sanar da nadin nasa a yau."
Wanene sabon mataimakin gwamnan Ondo?
Adelami ya yi ritaya a matsayin mataimakin magatakardar majalisar tarayya a watan Afrilun 2018. Ya fito daga yanki daya da marigayi tsohon gwamna Rotimi Akeredolu, karamar hukumar Owo.
Adelami ya yi takarar tikitin gwamnan APC a 2020 amma ya janyewa marigayi Akeredolu.
Aiyedatiwa ya kori yan majalisa da Akeredolu ya nada
A baya mun ji cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya rusa dukkan majalisar zartarwa a jiharsa, kamar yadda NTA News ta tattaro.
Gwamnan ya kuma rusa dukkan mukaman siyasa da suka hada da hadimai na musamman manya da kanana a jihar.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Ebenezer Adeniyan ya fitar a yau Laraba 24 ga watan Janairu.
Sanarwar ta bukaci dukkan wadanda aka sallama su mika takardun ofisoshinsu ga sakatarorin din-din-din a ma'aikatunsu.
Asali: Legit.ng