Kamar Kano, Mutane Sun Yi Cincirondo Wurin Tarban Gwamnan APC Bayan Hukuncin Kotun Ƙoli
- Dakta Nasir Idris ya samu tarba mai ban mamaki yayin da ya koma jihar Kebbi bayan Kotun Koli ta tabbatar masa da kujerar gwamna
- Magoya bayan APC daga dukkan kananan hukumomin jihar ne suka yi cincirindo tun daga filin jirgi domin murnar wannan nasara
- Da yake jawabi a ƙarshen ralin, Gwamna Idris ya buƙaci ƴan adawa su zo su haɗa kai da shi wajen ci da Kebbi gaba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi - Dubannin jama'a sun yi cincirindo a Birnin Kebbi jiya Lahadi domin murnar nasarar da Gwamna Nasir Idris (Ƙauran Gwando) ya yi a kotun ƙoli.
Magoya bayan jam’iyyar APC daga kananan hukumomi 21 na jihar Kebbi sun yi dandazo a Birnin-kebbi domin tarbar gwamnan yayin da ya koma jihar bayan yanke hukunci.
Jam'iyyar APC ce ta shirya wannan rali na musamman wanda ya fara daga filin jirgin Sir Ahmadu Bello domin murna da tarbar mai girma gwamna, cewar rahoton Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan baku manta ba Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da Nasir Idris na APC a matssyin sahihin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kebbi a 2023, The Cable ta tattaro.
Daga saukar gwamnan a filin jirgin, ayarin motocinsa da babura da sauran motocin magoya baya sun cika tituna, kana suka bi manyan titunan Birnin Kebbi.
Ƙauran Gwandu ya nemi haɗin kan ƴan adawa
Da yake jawabi ga cincirindon mutane bayan karkare ralin a filin wasa na Haliru Abdu, Gwamna Idris ya yi kira ga ‘yan adawa su zo a hada kai domin bunkasa jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa, idan har ƴan adawan dagaske suna siyasa ne don amfanin jama’a, yana gayyatar su taho su hada kai da shi domin ci gaban jihar Kebbi.
A cewarsa duk wasu matakai na shari'a da ake bi tun daga matakin kotun sauraron ƙararrakin zaɓe zuwa Kotun Ƙoli sun zo ƙarshe kuma da ikon Allah, "ni ne halastaccen gwamna."
Ya kuma jaddada aniyarsa na ci gaba da gudanar da ayyukan raya kasa da gwamnatinsa ta riga ta fara aiwatarwa wanda zai taɓa dukkan kananan hukumomin jihar 21.
Ya nemi goyon baya, fatan alheri, da addu’o’in jama’a ga gwamnatin APC, inda ya tabbatar da cewa zai cika dukkan alkawuran da ya ɗauka a kamfe na samar da cikakken tsaro ga al’ummar jihar.
Badaru ya yabawa Gwamna Namadi
A wani rahoton kuma Ministan tsaro, Muhammad Badaru, ya yabawa magajinsa na jihar Jigawa, Gwamna Umar Namadi bisa ayyukan da ya faro.
Badaru, tsohon gwamnan Jigawa ya ce a yanzu mutane sun gane gaskiyar abin da ya faɗa musu game da Ɗanmodi a lokacin kamfe.
Asali: Legit.ng