Jam'iyyar YPP Ta Rushe Tsarinta Cikin APC, An Bayyana Dalili
- Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, da wasu sanatoci sun tarbi dan takarar gwamna na jam'iyyar YPP a jihar Akwa Ibom, Bassey Albert zuwa APC
- Jaridar Legit ta tattaro cewa ya sauya shekar ne a ranar Juma'a, 19 ga watan Janairu a jihar Akwa Ibom dake kudu maso kudancin Najeriya
- Taron ya gudana ne a garin su Akpabio wato Ukana, dake yankin karamar hukumar Essien Udim
Jam'iyyar YPP ta sanar da rushe dukka tsarinta a jihar Akwa Ibom tare da narkewa a cikin jam'iyyar APC.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa sauyin shekar ya faru ne a ranar Juma'a, 19 ga watan Janairu 2024.
Sauya shekar yana da alaqa da yin mubaya'a ga shugaban majalisar dattawan kasar, Sanata Godswill Akpabio.
Akpabio ya tarbi masu sauya sheka daga YPP zuwa APC a Akwa Ibom
Jaridar Premium Times ma ta sanar da batun sauya shekar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda suka sauya shekar sun haɗa da, dan takarar gwamna na jam'iyyar ta YPP, Sanata Bassey Albert, da mataimakinsa AIG Asuquo Amba.
Sauran sune shugaban kwamitin zartarwa na jam'iyyar YPP a jihar, Nyeneime Andy da sauran su.
Yayin ziyarar da suka kaiwa shugaban majalisar dattawan, sun bayyana goyon bayansu ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyar APC gaba daya.
Sun kuma jaddada kudirin su na ci gaba da goyon bayan dukkan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a jihar, tare da kaucewa tsarin tafiya karkashin jam'iyyar YPP.
Da yake martani, Sanata Albert ya ce jam'iyyar ta yi maja da APC ne don marawa Shugaban kasa Tinubu baya tare da haɗa hannu da Akwa Ibom don ganin ba a samu rabuwar kai a jihar ba.
PDP ta taya gwamnan Ogun murna
Jam’iyyar PDP reshen jihar Ogun a daren Juma’a ta taya Gwamna Dapo Abiodun murnar lashe zaɓen gwamnan jihar kamar yadda Kotun Ƙoli ta tabbatar a ranar Juma’a.
Jam’iyyar PDP reshen jihar Ogun a daren Juma’a ta taya Gwamna Dapo Abiodun murnar lashe zaɓen gwamnan jihar kamar yadda Kotun Ƙoli ta tabbatar a ranar Juma’a.
Wani kwamitin alƙalai biyar na kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari’a John Okoro ya yanke hukuncin bai ɗaya, inda yi watsi da ƙarar da Oladipupo Adebutu ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar da ya gabata ya shigar.
Asali: Legit.ng