Gwamnan APC Ya Kori Kwamishinoni, SSG da Hadimansa Daga Aiki, Ya Bayyana Muhimmin Dalili 1

Gwamnan APC Ya Kori Kwamishinoni, SSG da Hadimansa Daga Aiki, Ya Bayyana Muhimmin Dalili 1

  • Gwamna Hope Uzodinma ya sallami dukkan muƙarrabansa daga aiko jim kaɗan bikin rantsar da shi karo na biyu a jihar Imo ranar Talata
  • Uzodinma ya gode wa kwamishinoni, SSG da sauran hadimai bisa gudummuwar da suka bada har ya samu nasara a zangonsa na farko
  • Ranar Talata, 16 ga watan Janairu, 2024 aka rantsar da Uzodinma karo na biyu a matsayin gwamnan Imo bayan samun nasara a zaben da ya gabata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Imo - Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo da yammacin jiya Talata, 16 ga watan Jamairu, 2024, ya rusa majalisar zartarwa ta jihar.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa waɗanda wannan mataki ya shafa sun haɗa da sakataren gwamnatin jihar Imo, dukkan kwamishinoni da masu ba da shawara ta musamman.

Kara karanta wannan

Gwamna Makinde ya bayyana abin da ya haddasa tashin abin fashewa a Ibadan, bidiyo ya bayyana

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma.
Gwamna Uzodinma Ya Rusa Majalisar Zartarwa Ta Jihar Imo Hoto: Hope Uzodinma
Asali: Twitter

Sauran sun kunshi manyan masu ba da shawara ta musamman, shugaban ma'aikatan gidan gwamnati da kuma sakataren watsa labaran mai girma gwamna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake rushe majalisar zartarwan, Gwamna Hope Uzodinma, ya gode wa muƙarrabansa bisa gudummuwar da suka bayar a zangon mulkinsa na farko.

A cewarsa, gudummuwarsu ce ta jagoranci gwamnatin ta samu nasara a shekaru huɗu na farko da ya kammala daga jiya Talata, 16 ga watan Janairu, Leadership ta rahoto.

Gwamnan ya ƙara da cewa ɗaukar wannan matakin ya zama dole don sake fasalin sabuwar gwamnatin da ya kafa a yanzu da nufin yin kyakkyawan aiki da sabon alkibla.

Uzodinma ya yi rantsuwa a karo na biyu

Wannan mataki na zuwa ne awanni bayan Uzodinma ya karɓi rantsuwar kama aiki karo na biyu a matsayin gwamnan jihar Imo.

Kara karanta wannan

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, kwamishina ya rasu kwanaki kaɗan bayan rasa muƙaminsa a arewa

An rantsar da gwamnan ne bayan samun nasara a zaben gwamnan da aka gudanar ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, sun halarci bikin rantsuwar.

Oshiomhole ya yi magana kan zaben Edo

A wani rahoton na daban Tsohon shugaban APC ya bayyana aniyarsu ta sake kwato jihar Edo daga hannun PDP a zaben gwamna mai zuwa a watan Satumba.

Adams Oshiomhole, tsohon gwamnan jihar ya ce dukkan masu ruwa da tsakin Edo sun maida hankali wajen yadda za a samu nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262