Bayan Nasara a Kotun Koli, Abba Gida-Gida Ya Ba Kwankwaso, Ganduje Da Gawuna Mukamai

Bayan Nasara a Kotun Koli, Abba Gida-Gida Ya Ba Kwankwaso, Ganduje Da Gawuna Mukamai

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mayar da hankali wajen aiwatar da wasu manufofin gwamnatinsa bayan Kotun Koli ta tabbatar da zabensa
  • Abba Gida-Gida ya kafa zauren dattawan Kano da zai kunshi manyan mutane da sukayi aiki a matakai daban-daban na tarayya da jiha
  • Wannan majalisa ta dattawa za ta dunga ba gwamnatinsa shawarwari kuma mambobinta za su zamana yan asalin jihar Kano

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa zauren dattawan jihar Kano domin ta zamo wata majalisa mai ba gwamnati shawara, rahoton Punch.

Wannan ci gaban na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Dawakin Tofa, ya gabatarwa manema labarai a ranar Asabar, 15 ga watan Janairu, rahoton The Sun.

Kara karanta wannan

Nasara a Kotun Koli: Abba Gida-Gida ya samu kyakkyawar tarba yayin da ya koma Kano ta hanyar Kaduna

Abba Kabir Yusuf ya kafa zauren dattawan Kano
Bayan Nasara a Kotun Koli, Gwamna Abba Gida-Gida Ya Kafa Zauren Dattawan Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa Allah ya albarkaci jihar da tarin dattawa da tsoffin shugabanni wadanda suka da suka samu nasarar gudanar da ayyukansu kuma ci gaba da kasancewa cikin koshin lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su wanene mambobin wannan zaure?

Zauren dattawan sun hada da tsoffin gwamnoni, mataimakan gwamnoni, shugabannin majalisar dattawa, kakakin majalisar wakilai, kakakin majalisar dokokin jiha, mataimakan kakakin majalisa.

Sauran sune alkalan Kotun Koli masu ritaya, alkalan kotun daukaka kara masu ritaya, tsoffin shugabannin alkalai na jihar, tsoffin sakatarorin dindindin na gwamnatin jihar.

Sai kuma tsoffin shugabannin ma'aikatan gwamnatin jihar wadanda dukkansu yan asalin jihar ne.

Kari a cikin zauren sune shugabannin Malamai, yan kasuwa, sarakunan gargajiya, tsoffin shugabannin tsaro daga jihar Kano, da sauran dattawan da gwamnati za ta dauko ta nada.

"Wadannan dattawan suna da ilimi, hikima, da gogewa, kuma gwamnatina za ta so ta amfani da kwarewarsu," inji gwamnan.

Kara karanta wannan

Abba vs Gawuna: Rundunar yan sandan Kano ta fitar da rahoton laifuka bayan hukuncin kotun koli

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, za a sanar da ranar rantsar da majalisar nan gaba.

Hakan na zuwa ne yan kwanaki bayan Kotun Koli ta tabbatar da Gwamna Yusuf a kan kujerarsa ta gwamnan jihar Kano tare da watsi da karar Nasir Gawuna na APC.

Kwankwaso kan batun shiga gwamnatin Tinubu

A wani labarin, mun ji cewa Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a zaben 2024, ya ce jam'iyyarsa da ya APC "za mu yi aiki tare a inda ya kamata mu taimaka masu mu taimaka masu, suma inda ya kamata su taimaka mana su taimaka mana".

Kwankwaso ya ce dangane da shiga gwamnatin APC mai mulki, “shiga gwamnati, toh ku bari idan lokacin ya yi sai mu gani."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng