Kano: Shugaban NNPP Ya Faɗi Gaskiyar Wanda Zai Samu Nasara Tsakanin Abba da Gawuna a Ƙotun Koli

Kano: Shugaban NNPP Ya Faɗi Gaskiyar Wanda Zai Samu Nasara Tsakanin Abba da Gawuna a Ƙotun Koli

  • Hashimu Dungurawa, shugaban NNPP na jihar Kano ya yi hasashen Abba Kabir Yusuf ne zai samu nasara a kotun koli yau Jumu'a
  • Legit Hausa ta tattaro muku cewa kotun koli ta tsara bayyana hukunci a shari'ar Kano da wasu jihohi ranar 12 ga watan Janairu
  • Gwamna Abba na fuskantar yiwuwar tsige shi daga kujerar mulki amma jiga-jigan NNPP sun nuna komai ka iya faruwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Kano, Hashimu Dungurawa, ya bayyana cewa jam'iyyar na sa ran samun nasara a hukuncin da kotun koli zata yanke.

Dungurawa ya yi wannan furucin ne yayin hira da jaridar Punch wanda aka wallafa da safiyar ranar Jumu'a, 12 ga watan Janairu, 2024 yayin da ake dakon hukuncin ƙarshe a kotun ƙoli.

Kara karanta wannan

Yusuf vs Gawuna: Sabon hasashe ya nuna wanda zai yi nasara a Kotun Koli a shari'ar Kano

Gwamna Abba da Nasir Gawuna.
Kano: Shugaban NNPP Ya Faɗi Gaskiyar Wanda Zai Samu Nasara Tsakanin Abba da Gawuna a Ƙotun Koli Hoto: Abba Kabir Yusuf, Dr Nasir Yusuf Gawuna
Asali: Facebook

Shugaban jam'iyyar mai kayan marmari ya ce NNPP na da kwarin guiwar cewa kotun kolin Najeriya zata yi adalci a hukuncin da zata yanke yau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasara ta mu ce da izinin Allah - NNPP

Ya ƙara da cewa jam'iyya mai mulkin jihar Kano ta ɗora fata da yaƙininta gaba ɗaya a hannun Allah.

A kalamansa, Dungurawa ya ce:

"Muna matuƙar farin ciki da Allah ya kawo ranar yanke hukunci gobe da safe (Jumu'a 12 ga watan Janairu). A wajen mu NNPP muna da kwarin guiwar za a yi adalci gobe.
"Shari'ar mu zata zama kwatankwacin ta shugaban ƙasa da kuma ta jihar Benuwai. Hukuncin ya ba su nasara saboda haka muna fatan muma haka zata faru gobe (yau) idan Allah ya yarda."

Bugu da kari, shugaban NNPP ya roki jama'a da kada su ji tsoro su nisanci tashin hankali, yana mai cewa:

Kara karanta wannan

Kano: Abubuwa 5 da ya kamata a sani yayin da Kotun Koli ke yanke hukunci kan shari'ar Abba da Gawuna

"Mu ƴan Kwankwasiyya an san mu mutane ne masu bin doka sau da ƙafa, a shirye muke mu bar zaman lafiya ya ɗore, babu tada yamutsi."

Wani mazaunin Kano kuma mamban NNPP ya shaida wa Legit Hausa cewa babu abinda ya gagari Allah, don haka sun miƙa lamarinsu gare shi a shari'ar da ke gaban Kotun koli.

Malam Sa'idu ya faɗa mana cewa:

"Muna nan muna jiran hukuncin da kotu zata yanke, mun san dai babu wanda zai iya canza abin da Allah SWT ya riga ya tsara zai faru. Abba muke fatan ya samu nasara."

Yusuf Babel, jigon APC a Kano ya faɗa mana cewa jiran rantsuwa kawai suke yi amma tun a hukuncin kotunan baya suka san cewa zasu samu nasara duk inda aka je.

Gwamnan Ogun da tawagarsa sun kama addu'a

A wani rahoton kuma Gwamna Dapo Abiodun da muƙarrabansa sun koma ga Allah yayin da kotun koli ke shirin yanke hukuncin kan zaben gwamnan Ogun

Jam'iyyar PDP ta ɗan takararta na gwamna, Ladi Adebutu ne suka ƙalubalanci nasarar gwamnan a gaban ƙuliya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262