Kotun Koli Ta Fara Karin Kummalo da Shari’ar Sanwo-Olu da Rhodes-Vivour

Kotun Koli Ta Fara Karin Kummalo da Shari’ar Sanwo-Olu da Rhodes-Vivour

  • Kotun Koli ta fara sauraron karar da jam'iyyar LP da PDP suka shigar kan zaben gwamnan jihar Legas, inda suke neman ya tsige Gwamna Sanwo-Olu
  • A yau Juma'a ne kotun za ta yanke hukunci kan rigingimun zaben gwamnonin Najeriya da aka gudanar a shekarar 2023
  • Akalla jihohi bakwai ne kotun za a yi zaman shari'arsu a yau da suka hada da Legas, Kano, Zamfara, Plateau, Ebonyi, Bauchi da Cross River

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Kotun Kolin ta fara yanke hukunci kan rigingimun zaben gwamnonin Najeriya da aka gudanar a shekarar 2023.

Wani kwamitin alkalai bakwai ke sauraron karar da aka shigar gaban kotun da ke kalubalantar sakamakon zaben gwamnan jihar Legas.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta ayyana wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Legas

Kotun koli ta fara da shari'ar zaben legas
Kotun Koli ta fara karin kummalo da shari’ar Sanwo-Olu da Rhodes-Vivour Hoto: @jidesanwoolu
Asali: Getty Images

Ana sa ran Kotun Kolin za ta yanke hukunci kan kararrakin gwamnoni bakwai da suka hada da Legas, Kano, Zamfara, Plateau, Ebonyi, Bauchi da Cross River.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun Koli ta fara sauraron shari'ar gwamnan Legas

Jam’iyyar Labour Party (LP) da dan takararta, Gbadebo Rhodes-Vivour, da PDP da dan takararta Abdulazeez Adediran, na kalubalantar nasarar Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Jam’iyyar LP ta bukaci Kotun Kolin da ta tabbatar da cewa an tabka kura kurai a zaben na ranar 18 ga watan Maris, da rashin bin dokar zabe, Daily Trust ta ruwaito.

Kotu ta tabbatar nasarar zaben Gwamna Sanwo-Olu

Hakazalika, Adediran ya shigar da hujjoji 34 na neman kotun ta soke hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Legas da kuma kotun daukaka kara, Rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Kotun Koli ta ayyana wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Bauchi

Mai shari’a Mohammed Garba Lawal ya karanta karar da dan takarar LP ya shigar na kalubalantar ayyana Sanwoolu na APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

A karshe Kotun Koli ta tabbatar da Gwamna Sanwo-Olu matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Legas, kamar yadda Legit ta tattara.

Kano: Abubuwa 5 da za ku sani gabanin hukuncin Kotun Koli

A yayin da ake jiran Kotun Koli ta yanke hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Kano, Legit Hausa ta tattaro wasu abubuwa 5 da ya kamata ku sani.

Abubuwan sun shafi yadda lamura ke wakana a jihar Kano, kama daga shirye shiryen yin zanga-zanga zuwa matakan da jami'an tsaro suka dauka a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.