Gwamnonin APC Sun Shiga Ganawa Mai Muhimmanci a Birnin Tarayya Abuja, Bayanai Sun Fito

Gwamnonin APC Sun Shiga Ganawa Mai Muhimmanci a Birnin Tarayya Abuja, Bayanai Sun Fito

  • Ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar APC na ganawar sirri yanzu haka a masaukin gwamnan jihar Imo da ke Asokoro a birnin tarayya Abuja
  • An gano cewa shugaban ƙungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ne ke jagorantar zaman yau Alhamis
  • Gwamnonin APC daga shiyyoyin ƙasar nan guda shida duk sun halarci wannan zama da rahotanni suka nuna har yanzu ba a gama ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwammonin da aka zaɓa karkashin inuwar All Progressive Congress (APC) sun shiga taron sirri yanzu haka a masaukin gwamnan jihar Imo da ke Asokoro a Abuja.

A rahoton jaridar Tribune Online, Gwamnan jihar Imo kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar APC, Hope Uzodinma, ne ke jagorantar taron yau Alhamis.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe kan takaddamar zaben gwamnan PDP, NNPP ta gurza kasa

Gwamnonin APC mai mulki.
Yanzun nan: Gwamnonin APC Sun Shiga Ganawa Mai Muhimmanci a Abuja, Bayanai Sun Fito Hoto: @Angelgabbyshara
Asali: Twitter

Jerin gwamnonin da suka halarci taron

Gwamnonin da suka halarci zaman sun haɗa da Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe da Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran waɗanda aka hanga sun shiga taron sune Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo, Gwamna Umar Namadi na Jigawa, Gwamna Mai Mala Buni na Yobe da Gwamna Francis Nwifuru na Ebonyi.

Ragowar gwamnonin da suka hallara sun ƙunshi Gwamna Ahmad Aliyu na Sakkwato, Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na Kwara, Gwamna Baseey Otu na Kuros Riba, Gwamna Dapo Abiodun na Ogun da dai sauransu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kotun kolin Najeriya ta fara yanke hukuncin ƙarshe kan kararrakin zaben gwamnonin da aka yi ranar 18 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya kori dukkan kwamishinoni da hadiman gwamnatinsa a arewa, ya faɗi dalili

Mafi akasarin gwamnonin da suka samu nasara a wannan zaɓe suna fuskantar shari'a a gaban kotu, inda abokan hamayyarsu ke kalubalantar nasarar da suka samu.

Kotun koli ta sa ranar yanke hukunci kan zaben jihohi 7

Rahotanni sun nuna cewa Kotun kolin Najeriya za ta yanke hukunci a kararrakin da aka shigar gabanta kan zaben gwamnonin jihohi 7 ranar Juma’a, 12 ga Janairu, 2024.

An gano cewa alƙalan kotun zasu fara zaman yanke hukuncin daga ƙarfe 9:00 na safe kuma taƙaddamar zaben Kano na cikin waɗanda za a ƙarƙare gobe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262