Rikicin Mulki: Yadda Mace Ta Hada Gwamna Fada da Mataimakinsa Har Ya Bar Duniya

Rikicin Mulki: Yadda Mace Ta Hada Gwamna Fada da Mataimakinsa Har Ya Bar Duniya

  • Doyin Odebowale ya zargi wata mace a gidan gwamnati da zama silar rikicin siyasar da aka shiga a Ondo
  • Tsohon hadimin na marigayi Rotimi Akeredolu ya ce hadimar uwargidar gwamna ce ta fito da sirrin lafiyarsa
  • Dr. Odebowale yake cewa wannan Baiwar Allah ta ci mana saboda Lucky Aiyedatiwa ya ba ta mukami

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Ondo - Tsohon mai taimakawa gwamnan Ondo da dabaru da harkoki na musamman Doyin Odebowale ya yi bayanin rikicin siyasar jihar.

Vanguard ta rahoto Dr. Doyin Odebowale yana karin haske a kan silar rigimar Lucky Aiyedatiwa da Marigayi gwamna Rotimi Akeredolu.

Akeredolu - Ondo
Marigayi Rotimi Akeredolu da sabon gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa Hoto:Lucky Aiyedatiwa, Rotimi Akeredolu
Asali: Facebook

Alakar Rotimi Akeredolu da Lucky Aiyedatiwa

Dr. Odebowale wanda ya yi aiki a matsayin hadimin Rotimi Akeredolu ya zargi mace da zama ummul-haba’isin sabanin da aka samu a mulki.

Kara karanta wannan

Ta fasu: Jerin sunayen 'yan siyasa 2 da ɗayansu ka iya zama sabon mataimakin gwamnan APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani bidiyo, mukarabbin tsohon gwamnan da ya riga mu gidan gaskiya ya ce da farko mai gidansa bai son jin kuskuren Lucky Aiyedatiwa.

Ondo: Ya aka yi aka fara rigimar mulki?

"Duk wanda ya kawowa marigayin aibin Aiyedatiwa da aka nada a yanzu, sai ya toshe shi.
Rashin jituwar Aiyedatiwa da Akeredolu ta fara ne da aka gano wata hadimar matar Akeredolu tana yada sirrin lafiyar gwamna da Aiyedatiwa.
Matar tana kutun-kutun domin zama mataimakiyar gwamna idan Akeredolu ya mutu.
Ina matar ta ke a yanzu? Tana tare da Lucky. Abin da ya batawa uwargidar gwamna rai shi ne matar ta rika yaudara kamar tana tare da Aketi.
Tana samun bayanin rashin lafiyar Aketi ta kai wa Lucky. Tana haduwa a Aiyedatiwa a Abuja a shirin zama mataimakiyar gwamna."

- Dr. Doyin Odebowale

Kara karanta wannan

Akeredolu: Fitaccen malamin addini ya fadi wanda zai zama gwamnan Ondo a 2024

Rashin lafiyar Akeredolu da cin amanar mutane

The Guardian ta rahoto Dr. Odebowale yana mai cewa Aketi bai kula da lafiyarsa da kyau ba, bai samun hutu, kullum yana sa hannu a takardu.

Tsohon hadimin yake cewa abokan aikinsa sun rika hana gwamnan ya huta, bai samun barci, ya ce nan gaba zai cigaba da bankado bayanai.

Odebowale ya ce Aketi yana fara rashin lafiya kawai aka fara maganar yaushe zai mutu, mutane suka fara taron yakar mutumin da ya kare su.

Gwagwarmayar da aka yi da Akeredolu

A lokacin rayuwarsa, an ji labari Rotimi Akeredolu ya gwabza da Miyetti Allah kuma ya yi fito-na-fito da yankin Arewa a lokacin zaben 2023.

Marigayi Akeredolu yana cikin wadanda aka gwabza da su da gwamnatin Muhammadu Buhari da cikin jam’iyyarsa ta APC mai-ci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng