'Dan Takarar Gwamnan Kuma Sanata Ya Bayyana Shirinsa Na Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC
- Magnus Abe, ɗan takarar gwamnan jihar Ribas a inuwar SDP a zaben 2023 ya tabbatar da jam'iyyar da zai koma a yanzu
- Tsohon sanatan ya bayyana cewa ƴan majalisa 27 na majalisar dokokin jihar Ribas sun tsira a yanzu amma akwai wata matsala
- A cewarsa, akwai wasu daga gefe da basu cikin yarjejeniyar da aka cimma a fadar shugaban ƙasa da zasu iya kawo cikas a kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP a zaben 2023 a jihar Ribas, Magnus Abe, ya ce zai fice daga jam’iyyar zuwa All Progressives Congress (APC) mai mulki.
Mista Abe, tsohon sanata a Najeriya ya bayyana haka ne a cikin shirin Siyasa a Yau na gidan talabijin din Channels ranar Litinin, 1 ga watan Janairu, 2024.
"A siyasance yanzu haka na kama hanyar komawa jam'iyyar APC," in ji tsohon mamban majalisar dattawan, Magnus Abe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abe, na kusa da shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya shiga takarar gwamna a jihar mai arzikin man fetur a ranar 18 ga watan Maris, amma ya sha kaye a hannun Siminalayi Fubara na jam'iyyar PDP.
Sai dai ya gaza zama minista daga jihar Ribas, maimakon haka shugaba Tinubu ya fi nutsuwa da Nyesom Wike, tsohon gwamnan da ya gabata, ya naɗa shi ministan Abuja.
Abe ya yi magana kan rikicin siyasar Ribas
Tsohon dan majalisar ya kuma yi la’akari da rikicin da ya dabaibaye jihar da kuma ficewar ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas su 27 daga PDP zuwa APC.
Abe ya yi kira da a rungumi zaman lafiya, inda ya ce duk da cewa an amince ‘yan majalisar su ci gaba da zama a jam'iyyar APC, amma akwai wasu daga gefe da ke kokarin kawo cikas a kotu.
A rahoton Daily Post, Sanata Abe ya ce:
"Kujerun ƴan majalisar sun tsole wa bangarori da dama ido, jam'iyyar PDP da suka baro tana kokarin ganin an dawo mata da kujerun. Shi kuma Gwamna ya amince su zauna a APC."
"Dangane da yarjejeniyar da aka cimma, ina ganin sun tsira a yanzu amma akwai wasu da ke can gefe, waɗanda ba su cikin yarjejeniyar kuma zasu kalubalanci batun a shari'a."
Tinubu ya bayyana burinsa guda ɗaya tal
A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya bayyana burinsa guda ɗaya tal wanda ya sa ya nemi kujerun mulki da dama har ya zama shugaban ƙasa.
Shugaba Tinubu ya faɗi sirrin ne a jawabinsa na shigowar sabuwar shekara 2024 wanda ya yi ranar Litinin, 1 ga watan Janairu.
Asali: Legit.ng