Kada Ku Fidda Rai, Komai Zai Daidaita a 2024, Ministar Jin Kai Ta Ba ’Yan Najeriya Kwarin Gwiwa

Kada Ku Fidda Rai, Komai Zai Daidaita a 2024, Ministar Jin Kai Ta Ba ’Yan Najeriya Kwarin Gwiwa

  • Gwamnatin Najeriya ta bayyana kadan daga abin da ta shiryawa talakawan kasa a cikin sabuwar shekarar da za a shiga
  • Minista Betta Edu ta ce 'yan kasa kada su fidda rai, akwai abubuwa masu kyau da gwamnati ta tsarawa talakawanta
  • 'Yan Najeriya na ci gaba da kukan bakin talauci, Atiku ya nemawa 'yan kasar sassauci wajen shugaban kasa Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Ministar jin kai ta Najeriya, Betta Edu ta karfafa gwiwar 'yan kasar, inda tace talakawa su kwantar da hankali abubuwa za su daidaita a sabuwar shekara.

Ta bayyana hakan ne a cikin sakon da ta fitar na taya 'yan kasa murnar shiga sabuwar shekarar 2024 mai kamawa nan da sa'o'i kadan, rahoton Vanguard.

Ta bayyana cewa, gwamnatin shugaba Tinubu ta kawo shirye-shirye da dama da za su fitar talakawa daga halin kaka-ni-kayi.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Zai Fito Ya Yiwa ’Yan Najeriya Don Sanin Abin da Zai Biyo Baya a 2024

Talakawa za su samu sauki a 2024, Betta Edu
Betta Edu ta karfafa gwiwar 'yan Najeriya kan 2024 | Hoto: edu_betta
Asali: Twitter

Hakazalika, ta yi tsokaci ga alkawarin shugaba Tinubu na tabbatar da an kawar da talauci a tsakanin 'yan Najeriya a lokacin da yake kamfe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda shirin gwamnati ke aiki

Ta kuma shaida yadda wasu daga cikin shirye-shiryen gwamnati da ke ofishinta da yadda aikinsu ke tasiri ga rayuwar 'yan Najeriya da yawa, jaridar Independent ta ruwaito.

Ta kara da cewa:

"Nan ba da jimawa ba, za mu fara shirye-shirye da yawa da za su ba ma'aikatar daman cimma manufarta, ciki har da kawo karshen yunwa, kange Najeriya da kuma wasu abubuwa mabambanta da za su cire 'yan Najeriya daga fatara."

Da take siffanta sabuwar shekara a matsayin sabon shafin rayuwa da ke dauke da fatan nasara da alheril minstar ta yiwa 'yan Najeriya fatan samun zaman lafiya da ci gaba.

Atiku ya nemi a yiwa takawan Najeriya sassauci

Kara karanta wannan

Dole gwamnatin tarayya ta magance matsin tattalin arziki a 2024, Atiku ya yi batu mai daukar hankali

A wani labarin, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bukaci gwamnatin tarayya da ta magance matsalar tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fama dashi a 2024, rahoton TheCable.

Atiku ya yi wannan kiran ne a sakonsa na sabuwar shekara ta 2024 ga al’ummar kasar a karshen makon nan.

Ya kuma siffanta 2023 a matsayin shekarar da ke cike da kalubale gareshi da ‘yan Najeriya, inda yace ya kamata kowa ya koyi darasi daga cikinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.