Shugaba Tinubu Zai Fito Ya Yiwa ’Yan Najeriya Don Sanin Abin da Zai Biyo Baya a 2024
- Gwamnatin Najeriya ta ce shugaban kasa Tinubu zai yiwa 'yan kasa jawabi a ranar Litinin 1 ga watan Janairun 2024
- Hakan na zuwa ne daidai lokacin da majalisa ta amince da kasafin kudin da shugaban ya ba ta tare da yin kari a kai
- Ana ci gaba da bayyana ta'ajibin yadda za a kashe wasu kudaden kasa wajen siyan littatafai ga 'yan majalisa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
FCT, Abuja - A gobe Litinin, 1 ga watan Janairun 2024 ne shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu na Najeriya zai fito a gidajen talabijin na kasar don yin jawabi.
Legit ta samu labari daga fadar shugaban kasa cewa, zai yi jawabin ne ga 'yan Najeriya da misalin karfe 7 na sanyin safiyar ranan.
A cikin wata sanarwa da aka fitar dauke da sa hannun hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, an ce za a yada jawabin Tinubu a gidajen talabijin da rediyo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hasashen abin da Tinubu zai yi magana a kai
Ana kyautata zatin cewa, shugaban zai yiwa 'yan Najeriya barka da shiga sabuwar shekara tare da bayyana wasu shirye-shiryen da gwamnatinsa ke yi wajen tabbatar da ci gaban kasa.
Daga hawan shugaban kasa Tinubu 'yan Najeriya ke koka yadda ya janye tallafin man fetur, kasar na ci gaba da fuskantar yanayi mai kama da dagulewar tattalin arziki.
Babban abin da 'yan kasar suka fi mai da hankali a kai kwanan nan shine yadda darajar kudin kasar; Naira ke ci gaba da lalacewa tun hawan Tinubu.
An amince da kasafin 2024
Za a shiga sabuwar shekarar ne dai a daidai lokacin da majalisar kasar ta amince da kasafin kudin da Tinubu ya mika mata.
Rahotanni a baya sun nuna yadda majalisar ta yi kari kan wasu abubuwan da ke cikin kasafin kudin da ya bayar.
Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da cece-kuce kan kare-kare da kashe kudaden da ke cikin kasafin na shekara mai zuwa.
Za a siyawa 'yan majalisa littatafan Naira biliyan 3
A bangare guda, an ware Naira biliyan 3 don siyan litattafai na dakin karatun majalisar dokokin Najeriya a kasafin kudin 2024.
Wannan yana kunshe ne a cikin lissafin kasafi na 2024 da majalisar ta amince dasji a jiya Asabar 30 ga watan Disamba, The Cable ta ruwaito.
Kamar yadda bayanin kasafin kudin ya nuna, an kuma ware Naira biliyan 12.12 don hidimar dakin karatu na majalisar dokoki ta kasa.
Asali: Legit.ng