Abba vs Gawuna: An Yi Zanga-Zanga a Kano Kan Takaddamar Zaben Gwamna
- Dubban magoya bayan jam'iyyar NNPP sun gudanar da zanga-zanga a karamar hukumar Rogo ta jihar Kano
- Magoya bayan jam'iyyar su Abba Gida-Gida sun yi zanga-zanga ne don neman kotun koli ta yi gaskiya a yayin yanke hukunci a takaddamar zaben gwamnan jihar
- Sai dai kuma, zanga-zangar ta rikida ta koma rikici bayan da wasu mutane suka kona wata abar hawa
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Kano - Dubban mutane da ake zaton magoya bayan jam’iyyar NNPP ne, sun mamaye tituna a ranar Asabar, 30 ga watan Disamba, don zanga-zanga kan takaddamar zaben gwamna tsakanin gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, da takwaransa na APC, Nasir Gawuna.
A cewarsu, suna son kotun koli ta yanke hukunci na gaskiya don tabbatar da muradin mutanen Kano kan Yusuf.
Magoya bayan NNPP sun yi taron addu'a a Kano
Masu zanga-zangar sun mamaye unguwanni a karamar hukumar Rogo da ke jihar a ranar Asabar. Sun fara ne da addu’an neman zabin Allah, rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan taron addu’an, sai suka yi tattaki, dauke da kwalaye da rubutu iri-iri.
Zanga-zangar ya rikida ya koma hargitsi yayin da wasu mutane suka cinnawa wata mota wuta a unguwannin.
Tuni dai'yan sanda suka hana duk wani taron siyasa ko zanga-zanga a ciki da wajen babban birnin.
A ranar 21 ga Disamba, 2023, Kotun Koli ta tanadi hukunci a karar da Yusuf ya shigar, yana kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara da kotun sauraren kararrakin zabe ta jihar da suka tsige shi daga mukaminsa tare da bayyana Gawuna a matsayin wanda ya yi nasara.
Kwamitin kotun mai mutane biyar karkashin jagorancin mai shari’a John Okoro, ya tanadi hukuncin ne bayan da bangarorin suka yid an takaitaccen muhawara.
Kano: Gwamna Abba ya damƙa ƙananan yara 7 hannun Iyayensu bayan ceto su, ya tura saƙo ga gwamnan Bauchi
Legit Hausa ta zanta da wani masoyin Abba Gida Gida mai suna Muhammad Sani inda ya bayyana cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba har sai sun ga an yi wa gwamnan na Kano adalci.
Sani ya ce:
“Za mu ci gaba da hada su da Allah, babu abun da ya fi kafrfin Allah kuma mulki nasa ne shi ya bai wa Abba don haka ba zai bari wasu su yi masa fin karfi ba.
“Muna kara kira ga alkalan kotun koli a kan su yi gaskiya sannan su ji tsoron Allah yayin yanke hukunci. Abba dai shine zabinmu mu Kanawa. Da izinin Allah shi ne zai tabbata a kan kujerar gwamnan Kano kuma sai ya yi takwas.”
Jigo ya yi hasashen hukuncin zaben Kano
A wani labarin kuma, mun ji cewa Razaq Aderibigbe, babban jigon New Nigeria People's Party (NNPP) ya bayyana yaƙinin cewa kotun koli zata tabbatar da zabin al'ummar jihar Kano.
Mista Aderibigbe ya ce alamu sun nuna cewa alkalan kotun kolin Najeriya mutane ne masu gaskiya, waɗanda zasu yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da adalci da daidaito.
Asali: Legit.ng