Apapa: Sabon Rikici Ya Ɓalle a Jam'iyyar Adawa Yayin da Aka Lakaɗa Wa Wasu Jiga-Jigai Duka

Apapa: Sabon Rikici Ya Ɓalle a Jam'iyyar Adawa Yayin da Aka Lakaɗa Wa Wasu Jiga-Jigai Duka

  • Alamu sun nuna rigimar cikin gida ta ƙara dabaibaye jam'iyyar Labour Party ta ƙasa bayan lakaɗa wa wasu jiga-jigai duka a Edo
  • Jami'an LP biyu da ake zato ƴan tsagin Lamidi Apapa ne sun ci na jaki a hannun wasu mutane a Benin yayin da suka je wani aiki
  • Kakakin LP na jihar Edo, Samson Uroupa, ya ce babu wani tsagi a jam'iyyar domin kotun ƙoli ta raba gardama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Rigingimun da suka dabaibaye Labour Party (LP) ta kasa ya ƙara tsanani yayin da aka yi wa wasu shugabanni biyu dukan kawo wuƙa a jihar Edo.

Rahoton Vanguard ya nuna cewa ranar Jumu'a, manyan jam'an LP guda biyu, Anslem Eragbe, da wani da ba a gano sunansa ba sun ci na jaki hannun wasu mutane.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai mummunan hari, sun kashe malami tare da sace bayin Allah sama da 35

Lamidi Apapa, shugaban tsagin LP.
Sabon rikici ya balle a jam'iyyar LP yayin da aka lakaɗawa jiga-jigai duka a Edo Hoto: Lamidi Apapa
Asali: Twitter

A faifan bidiyon da ke yawo an ga mutanen suna dukan jiga-jigan biyu a wani wuri da ba a bayyana ba amma ana ganin motoci da gidaje a kewayen wurin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ga mutane kusan biyar sun taru suna dukan Mista Eragbe da kafafunsu da wasu abubuwa, sun yaga masa tufafin da ke jikinsa farare, sun bar shi da ƙaramin wando.

Shi kuma ɗayan jigon wanda ya sa shuɗin tufafi na zaune a ƙasa wasu mutane sun kewaye shi, Leadership ta ruwaito.

An tattaro cewa sun ziyarci Benin, babban birnin jihar Edo ne domin aiwatar da tsarin ɓangaren LP ta ƙasa karkashin jagorancin Lamidi Apapa, a shirin zaben fidda gwani.

LP ta maida martani kan abinda ya faru a Edo

Da yake tsokaci kan lamarin, kakakin LP na jihar Edo, Samson Uroupa, ya bayyana mutanen biyu, waɗanda yace ba mambobin LP bane da mayaudara.

Kara karanta wannan

Yanzu aka fara: Miyagu sun yi alkawarin sake kai hari bayan kashe mutum 195 a Filato

A cewarsa, dukkansu ba su da alaƙa da jam'iyyar LP kuma sun zo ne da nufin haddasa fitina da tada zaune tsaye.

Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro a jihar da su kama duk wanda ke da’awar wani bangare a jam’iyyar LP, yana mai cewa kotun koli ta warware wannan matsalar.

A kalamansa ya ce:

"Muna ganin idan har yanzu akwai wanda ke da’awar wani bangare a jam’iyyar, to ya kamata jami’an tsaro su kamo irin wadannan mutane domin kotun koli ta yanke hukunci."

Kano: Ciyamomi 44 sun kai Abba kara kotu

A wani rahoton na daban Taƙaddama ta barke tsakanin kananan hukumomi 44 na jihar Kano da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP.

Ciyamomi 44 sun shigar da ƙara a gaban babbar kotun tarayya a Abuja suna neman a hana gwamnatin Kano amfani da kuɗinsu a ginin gadoji 2.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262