Ta Fasu: Jerin Sunayen Ƴan Siyasa 2 da Ɗayansu Ka Iya Zama Sabon Mataimakin Gwamnan APC

Ta Fasu: Jerin Sunayen Ƴan Siyasa 2 da Ɗayansu Ka Iya Zama Sabon Mataimakin Gwamnan APC

  • An sake shiga ruɗani da rashin tabbas kan naɗa sabon mataimakin gwamna a jihar Ondo amma dai gwamna na ta laluben wanda ya dace
  • Legit Hausa ta ruwaito cewa Lucky Aiyedatiwa ya karɓi rantsuwar kama aiki a matsayin gwamnan jihar Ondo ranar Laraba, 27 ga watan Disamba
  • Wannan ya biyo bayan mutuwar Gwamna Oluwarotimi Akeredolu, bayan ya yi fama da doguwar jinya a ƙasar Jamus

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya fara lalube da binciken wanda zai ɗauko a matsayin mataimakin gwamna, Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito ranar Jumu'a, 27 ga watan Disamba, Gwamna Aiyedatiwa ya fara faɗi tashin neman wanda zai taya shi shugabanci.

Kara karanta wannan

2024: Kwanaki 2 da mutuwar gwamna, Lucky ya manta da shi ya ziyarci Tinubu kan wani babban dalili

Gwamna Aiyedatiwa na jihar Ondo.
Ondo: Jerin Manyan Yan Siyasa Biyu Da Ka Iya Zama Mataimakin Gwamnan Ondo Hoto: Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Ondo: Har yanzu Aiyedatiwa na farautar mataimaki

Wata majiya mai tushe daga ofishin sabon gwamnan ta bayyana cewa da yiwuwar Aiyedatiwa ya ɗauki ɗaya daga cikin mambobin majalisar zartarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ƙara da cewa tuni gwamnan ya fara ganawa da masu ruwa da tsaki na siyasa a ciki da wajen jihar Ondo domin zakulo wanda ya dace kuma mai ɗa'a a matsayin mataimakin gwamna.

A cewar majiyar, Gwamna na dubawa tare da nazari don ɗauko mataimaki daga mazaɓar Sanatan Ondo ta arewa ko ta tsakiya. APC ke jan ragamar jihar Ondo.

Majiyar ta ambaci waɗanda ake hangen zasu iya zama mataimakin gwamnan wanda ya haɗa da shugaban ma'aikata na tsohon gwamnan jihar, Olugbenga Ale da kwamishinan makamashi.

A rahoton The Nation, majiyar ta ce:

"Nan da ƴan kwanaki za a sanar da sunan sabon mataimakin gwamna, har yanzu gwamna na laluben wanda zai zama mai biyayya da taimaka masa."

Kara karanta wannan

Karin hadiman gwamna 2 sun yi murabus daga muƙamansu, sun bayyana babban dalili

"Da yiwuwar zai ɗauki ɗaya daga cikin waɗanda suka fi masa biyayya a lokacin gwamnatin marigayi Gwamna Akeredolu."
"Har yanzu yana ta taruka da shugabannin jam'iyyar APC na shiyyar sanatan Ondo ta kudu kan wannan batu."

Yan siyasa biyu da ka iya zama mataimakin gwamnan Ondo

1. Razak Obe

2. Olugbenga Ale.

Gwamnan PDP Zai Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC

A wani rahoton kuma Wani fitaccen malamin addini a jihar Legas, Primate Elijah Ayodele, ya ce Gwamna Siminalayi Fubara na Ribas zai tsallaka zuwa APC.

Legit Hausa ta tattaro Primate Ayodele na cewa wannan shiri na 'sauya sheƙa' wani ɓangare ne na babban kullin kawar da jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262