Gwamma Lawal Ya Kafa Tarihi, Ya Yi Abinda Ba a Taba Gani Ba Tunda Aka Kirkiro Jihar Zamfara
- Dauda Lawal ya kafa tarihin zama gwamna na farko da ya fara biyan ma'aikatan gwamnati albashi wata 13 a shekara ɗaya a Zamfara
- Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a Gusau
- Ya ce ƙarawa ma'aikata albashin wata ɗaya ya nuna kudirin gwamna na inganta walwala da jin daɗin ma'aiktan gwamnati
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal ya biya ma'aikatan gwamnati albashin watan 13 a jihar Zamfara, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da yanke shawarar biyan ma'aikata albashi na watan 13 ranar Alhamis, 28 ga watan Disamba, 2023.
Wannan mataki ne kunshe a wata sanarwa da shugaban hukumar kula da ma'aikatan jihar, Ahmed Aliyu Liman, ya fitar, cewar rahoton Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An taba biyan albashin wata 13 a Zamfara?
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ya bayyana cewa Dauda Lawal ya kafa tarihin da ba a taɓa yi ba a jihar Zamfara.
Kakakin gwamnan ya ce biyan ma'aikata albashin wata na 13 shi ne karo na farko da aka taɓa yi a tarihin jihar Zamfara da ke Arewa Maso Yamma.
A cewarsa, matakin ya yi daidai da kudurin gwamnatin jihar na kyautata jin dadi da walwalar ma’aikata da kuma zaburar da su yi kyakkyawan aiki yadda ya kamata.
Bala Idris ya ce:
"A yau ne Gwamna Dauda Lawal ya amince a gaggauta biyan alawus-alawus na karshen shekara ga ma’aikatan gwamnati a jihar Zamfara."
"Irin wannan karimcin ana yinsa ne da nufin kara wa ma’aikata kwarin gwiwa da kuma ba su tallafin kudi a lokacin hutu.
“Yana da kyau kowa ya san cewa wannan shi ne karo na farko a tarihin Zamfara da gwamnatin jihar ta fara biyan ma’aikata albashin watanni 13 cikin shekara ɗaya."
"Wannan matakin ya nuna muradin Gwamna Lawal na aiwatar da tsare-tsare da zasu inganta yanayin aiki, karin albashi, da samar da damarmaki ga ma’aikatan gwamnati."
PDP ya jaddada matsaya kan sauya sheƙar yan majalisa 26
A wani rahoton kuma Jam'iyyar PDP ta ce ba gudu ba ja da baya kan kujerun ƴan majalisa 26 da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a jihar Ribas.
Adeyemi Ajibade (SAN), bai bada shawara kan shari'a na PDP ya ce duk da Tinubu ya warware rikicin Ribas amma ƴan majalisar sun rasa kujerunsu.
Asali: Legit.ng