Babban Jigo Ya Bayyana Kujerar Gwamnan APC da Kotun Koli Za Ta Ƙwace Ta Bai Wa Jam'iyyar PDP
- Ladi Adebutu ya bayyana kwarin guiwar cewa kotun koli zata kwace mulki daga Gwamna Abiodun, ta tabbatar masa da nasara
- Ɗan takarar gwamnan jihar Ogun a inuwar PDP a zaɓen 2023 ya faɗi haka ne a sakon kirsimeti da ya fitar ranar Litinin
- Ya buƙaci mutanen jihar Ogun su yi farin ciki tare da sanya yaƙini a zuƙatansu cewa kotun koli zata yi adalci
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ogun - Ɗan takarar gwamnan jihar Ogun a inuwar Peoples Democratic Party (PDP), Ladi Adebutu, ya ce ya ɗaukaka kara zuwa kotun koli domin kwato haƙƙinsa.
Mista Adebutu ya ce tuni ya fara bin matakan da suka dace na shari'a, "domin kwato hakkinsa da mutanen jihar Ogun suka ɗora masa a kotun koli cikin ruwan sanyi."
Adebutu yana kalubalantar nasarar Gwamna Dapo Abiodun na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A watan Satumba, mai shari'a Hamidu Kunaza na kotun ɗaukaka ƙara ya kori ƙarar ɗan takarar PDP bisa rahin cancanta, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Kotun koli zata yi adalci - Adelubu
A sakon kirsimeti da mai magana da yawunsa, Afolabi Orekoya, ya fitar ranar Litinin, 25 ga watan Disamba, 2023, Adebutu ya ce tuni ya ɗaukaka ƙara zuwa kotun koli, vanguard ta tattaro.
Ya kuma buƙaci ɗaukacin al'ummar jihar da suka kaɗa kuri'a da su, "tsaya tsayin daka kuma su sa a ransu cewa adalci da gaskiya zasu bayyana a kotun ƙoli."
Tsohon ɗan majalisar wakilan tarayya ya ƙara da cewa farin ciki da murnar zuwan kirsimeti, "Alama ce da kwarin guiwar nasarar da zamu samu a kotun Allah ya isa."
"Muna kara godiya mara adadi da kuma farin ciki mara misaltuwa da muke samu daga al'ummar faɗin jhar nan, mutanen Ogun sun yi imanin za a a yi adalci a kotun ƙoli."
"Muna rokon ku da ku yi murna cikin lumana, ku yi murna tare da 'yan uwa da abokan arziki da fatan masararmu ta kusa."
Tinubu ya tura sako ga shugaban APC
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya taya shugaban APC murnar ƙarin shekara yayin da ake jiran hukuncin kotun koli kan zaben Kano.
Shugaban ya bayyana Ganduje a matsayin cikakken aboki mai biyayya kuma amini wanda ya kasance kwararren ɗan siyasa.
Asali: Legit.ng