Kotun Koli Na Shirin Yanke Hukunci Kan Zaben Kano, Shugaba Tinubu Ya Aike da Sako Ga Ganduje

Kotun Koli Na Shirin Yanke Hukunci Kan Zaben Kano, Shugaba Tinubu Ya Aike da Sako Ga Ganduje

  • Bola Ahmed Tinubu ya taya shugaban APC murnar ƙarin shekara yayin da ake jiran hukuncin kotun koli kan zaben Kano
  • Shugaban ya bayyana Ganduje a matsayin cikakken aboki mai biyayya kuma amini wanda ya kasance kwararren ɗan siyasa
  • Ya kuma yi masa fatan alheri da ci gaba da zama cikin ƙoshin lafiya, yana mai cewa kar ya dakata a kokarinsa na yi wa ƙasa hidima

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aike da saƙon taya murna na ƙarin shekara ga shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Shugaban Tinubu ya taya Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano murnar cika shekara 74 a duniya, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Shugaba Tinubu ya tilasta Gwamna Fubara sa hannu kan yarjejeniya? Shugaban PDP ya fadi gaskiya

Shugaba Tinubu ya taya Ganduje murnar cika shekara 74 a duniya.
Shugaba Tinubu Ya Taya Ganduje Murnar Cika Shekara 74 a Duniya Hoto: Dr Abdullahi Umar Ganduje, Ajuri Ngelale
Asali: Facebook

Da yake jinjinawa irin halayen tsohon gwamnan, Tinubu ya bayyana Ganduje a matsayin mai kishin dimokradiyya, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’umma hidima da kuma Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Litinin, 25 ga watan Disamba, 2023.

Sakon da Tinubu ya aike zuwa ga Ganduje

Shugaba Tinubu ya bayyana shugaban jam'iyya mai mulkin a matsayin aboki mai tsananin biyayya kuma amintaccen amininsa.

A kalamansa, Asiwaju ya ce:

"Ina taya shugaban jam'iyyar mu ta kasa murnar cika shekaru 74 a yau. Dakta Abdullahi Ganduje dan siyasa ne kuma kwararren ma'aikacin gwamnati wanda ya ɗare matakin kololuwa."
"A tarayyata da shi, Ganduje ya nuna shi aboki ne nagari kuma amini. Yana sadaukar da duk abin da yake da shi, tare da mai da hankali wajen tabbatar da an aiwatar."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Zanga-zanga ta ɓarke a gidan gwamnatin jihar PDP kan muhimmin batu

"Yadda yake tafiyar da jam’iyyar mu tun da ya zama shugaban APC na kasa, shaida ce ta tabbatar da irin kwazonsa a matsayinsa na ƙwararren ɗan siyasa.”

Yayin da yake yi wa Ganduje fatan alheri da kuma koshin lafiya, Tinubu ya roki shugaban jam’iyyar APC na kasa da kada ya yi kasa a gwiwa wajen yi wa Nijeriya hidima, Premium Times ta tattaro.

Wannan sakon taya murnar ƙarin shekara na zuwa ne yayin da kotun koli ke shirin raba gardama tsananin APC da NNPP a zaben gwamnan Kano.

Moghalu ya caccakin tsohon gwamman CBN

A wani rahoton kun ji cewa Tsohon gwamnan babban banki, Kingsley Moghalu, ya ayyana Godwin Emefiele a matsayin mafi munin gwamnan CBN a tarihin Najeriya

A wani sako da ya wallafa a shafinsa ranar Asabar, 23 ga watan Disamba, Moghalu ya feɗe lokacin Emefiele a CBN.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262