Shari'ar Zaben Kano: Ina Da Tabbacin Samun Nasara, Abba Kabir Ya Magantu, Ya Roki Kanawa
- Yayin da ake dakon hukuncin shari'ar gwamnan jihar Kano, Gwamna Abba Kabir ya bayyana kwarin gwiwarsa
- Abba Kabir ya ce ya na da tabbacin samun nasara a hukuncin da za a yanke a Kotun Koli kan shari'ar zaben gwamnan jihar
- Gwamnan ya bayyana haka ne a jiya Lahadi 24 ga watan Disamba a filin wasa na Sani Abacha yayin bikin horas da matasa 2,500 a jihar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya bayyana kwarin gwiwarsa kan hukuncin Kotun Koli.
Abba Kabir ya bayyana haka ne a jiya Lahadi 24 ga watan Disamba a filin wasa na Sani Abacha yayin bikin horas da matasa 2,500 a jihar.
Mene Abba Kabir ke cewa kan shari'ar?
Gwamnan ya yabawa alkalan kan yadda suka doge don ganin sun yi adalci kan shari'ar da ke gabansu, cewar Daily Nigerian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kirayi jama'ar jihar da su kwantar da hankalinsu da kuma kara musu karfin gwiwa kan alkalan kotun.
Ya ce:
"Ina amfani da wannan dama don yabawa alkalan Kotun Koli wurin dogewarsu kan tabbatar da adalci a hukuncin.
"Ina kuma kira ga jama'a da su kwantar da hankalinsu kan shari'ar alkalan kotun da kuma amincewa da gaskiyarsu."
Wane tabbaci Abba Kabir ya bai wa 'yan jihar?
Abba Kabir ya tabbatar wa magoya bayansa cewa ya na da tabbacin samun nasara a shari'ar da za a yanke.
Wannan na zuwa ne bayan rusa zaben gwamnan da kotun zabe da ta Daukaka Kara suka yi a baya, cewar Daily Post.
"Kada ka tsoma baki a kitimurmurar da ke tsakanin Abba da Gawuna a Kano", Dattijan Yarbawa ga Tinubu
Gwamnan ya sake daukaka kara zuwa Kotun Koli inda a ranar Alhamis 21 ga watan Disamba ta tanadi hukunci.
Hukunce-hukuncen kotu da suka ba da mamaki a 2023
A wani labarin, tun bayan zaben 2023 'yan takara da dama suka runtuma kotu don kalubalantar zaben.
An yi hukunce-hukunce da dama a 2023 wadanda suka ba da mamaki da kuma bazata.
Wannan rahoton ya jero muku manya-manyan hukunce-hukuncen da aka yi a shekarar 2023 da suka ba da mamaki.
Asali: Legit.ng