"Ba Ka Jefa Al'umma Cikin Wahala Ba", Babangida Aliyu Ya Yaba Da Salon Mulkin Uba Sani a Kaduna

"Ba Ka Jefa Al'umma Cikin Wahala Ba", Babangida Aliyu Ya Yaba Da Salon Mulkin Uba Sani a Kaduna

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Neja kuma Shugaban Gidauniyar Tunawa da Sardauna, Babangida Aliyu ya yabawa Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna saboda salon mulkinsa mai ban sha'awa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Mista Aliyu yayin ziyara da ya kai wa gwamnan a ranar Asabar a Kaduna, ya ce salon mulkin Sani na tafiya tare da kowa ba tare da jefa al'umma cikin wahala ba abin yabawa ne.

Tsohon gwamnan ya jagoranci wata tawaga mai karfi daga Gidauniyar Tunawa da Sardauna zuwa ziyara ta musamman gidan Sir Kashim Ibrahim, Kaduna don ta'aziyya bisa abin bakin ciki da ya faru a Tudun Biri, Karamar Hukumar Igabi.

Mista Aliyu ya jinjinawa gwamnan bisa saman nasarar aiwatar da ayyukan cigaba a jihar ta Kaduna. Ya ce abin lura ne ganin yadda aka aiwatar da ayyukan ba tare da jefa mutane cikin kunci ba, duk da kallubalen tattalin arziki a kasar.

Kara karanta wannan

Ana ta shirin yanke hukunci, Kanawa sun yi wa Abba Gida-Gida babbar tarba a jihar Kano

Aliyu ya kara da cewa:

"Dole in yaba wa Gwamna Sani bisa ware fili hekta 100 don aikin Jami'ar Hadin Kan Arewa, wacce Gidauniyar Tunawa da Sardauna ke cikin aikin. Wannan bada filin babban mataki ne bisa cigaban yankin baki daya."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164