Ganduje Ya Yi Babban Kamu, Ɗan Majalisar Arewa Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC
- Ɗan majalisar dokokin jihar Neja mai wakiltar mazaɓar Katcha, Yakubu Bala ya sauya sheƙa daga jam'iyyar SDP zuwa jam'iyar APC mai mulki
- Mista Bala ya tabbatar da hake ne yayin zaman majalisar na ranar Laraba, 20 ga watan Disamba, 2023 amma bai faɗi dalilin da ya sa ba
- Kakakin majalisar dokokin jihar Neja, Abdulmalik Sarkindaji, ya yi masa maraba zuwa APC tare da roƙon ya mara wa gwamnati baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Niger - Mamba a majalisar dokokin jihar Neja da ke shiyyar Arewa ta tsakiya, Mista Yakubu Bala, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a hukumance.
Ɗan majalisar jihar mai wakiltar mazaɓar Katcha a majalisar dokokin ya tabbatar da ɗaukar matakin ficewa daga jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) zuwa APC.
Bala ya sanar da sauya shekarsa ne a zaman majalisar dokokin jihar Neja ranar Laraba, 20 ga watan Disamba, 2023, kamar yadda jaridar The Nation ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa ɗan majalisar ya koma APC?
Sai dai ɗan majalisar bai bayyana ainihin dalilin da ya sa ya zaɓi sauya sheka daga SDP wadda ya ci zaɓe karkashinta zuwa APC mai mulkin ƙasar nan ba.
Da yake maratani kan wannan ci gaban, kakakin majalisar dokokin jihar Neja, Honorabul Abdulmalik Sarkindaji, ya yi wa Yakubu Bala maraba da zuwa jam'iyyar APC.
Kakakin majalisar ya kuma buƙace shi da ya mara baya ga kokarin gwamnatin jihar Neja na samar da romon demokaraɗiyya ga al'ummar jihar ba tare da nuna wariya ba.
Jam'iyyar APC ta fara shirin tunkarar zaben 2027
Wani cikakken mamban APC a jihar Katsina, Malam Adamu Mahmud, ya shida wa Legit Hausa cewa jawo hankalin ƴan adawa na ɗaya daga cikin abinda suka sa a gaba.
A kalamansa ya ce:
"Wannan ci gaba ne mai kyau, bari na faɗa maka mu a APC muna maraba da kowa, kuma muna nan muna kokarin shawo kan wasu yan majalisu su baro jam'iyyunsu."
"Ba zan faɗa maka sunayensu ba sai loƙaci ya yi, amma akwai jiga-jigai a PDP da muke kokarin su shigo APC a Katsina gabanin zaɓen 2027."
Shugaba Tinubu ya naɗa alƙalai 11 a kotun koli
A wani rahoton na daban Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci majalisar dattawan Najeriya ta amince da naɗin sabbin alƙalai 11 da zasu koma aiki a kotun koli.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya karanto wasiƙar buƙatar Shugaba Tinubu a zaman sanatoci na ranar Laraba, 20 ga watan Disamba, 2023.
Asali: Legit.ng