To Fah: Fitaccen Malami Ya Ayyana Shiga Tseren Takarar Gwamna a Jihar PDP, Ya Faɗi Dalili

To Fah: Fitaccen Malami Ya Ayyana Shiga Tseren Takarar Gwamna a Jihar PDP, Ya Faɗi Dalili

  • Wani malamin addinin kirista ya ayyana shiga tseren takarar gwamnan jihar Edo a zaɓe mai zuwa na shekarar 2024
  • Rabaran Andrew Obinyan ya bayyana cewa al'ummar jihar da wasu ƴan Najeriya masu kishi ne suka matsa masa lamba ya fito takara
  • Sai dai a hirar da ya yi a sakatariyar kungiyar NUJ da ke Benin, limamin cocin bai bayyana jam'iyyar da zai tsaya takarar ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Wani limamin cocin Katolika, Rabaran Andrew Obinyan, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a jihar Edo a zaben gwamnan jihar mai zuwa a 2024.

Rabaran Obinyan shi ne limamin cocin St Francis Catholic Church da ke Benin, babban birnin jihar Edo, kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Fitaccen malamin addini ya yi hasashen makomar Najeriya ana tsaka da wahala

Malamin coci ya fito takara a Edo.
Malamin Addini Ya Shiga Tseren Takarar Gwamnan Jihar Edo a Zaben 2024 Hoto: BBM Home Of News/facebook
Asali: Facebook

Fitaccen Malamin addinin kiristan ya ce ya shiga tseren takara ne bayan kiraye-kiraye da kuma matsin lamba daga mutanen Edo masu kishin kasa da kuma ‘yan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, al'umma jihar da kuma wasu ƴan Najeriya masu kishin ƙasa ne suka matsa masa lamba da rokon ya shiga takarar gwamna a zaɓe mai zuwa.

Ya bayyana aniyarsa ta shiga takarar ne ranar Litinin, 18 ga watan Disamba, 2023 sa'ilin da ya kai ziyara sakateriyar kungiyar ƴan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Edo a Benin.

A kalamansa ya ce:

"Kasancewa ta kwararren limamin majami'a, na shirya tsaf domin yi wa al'ummar jihar Edo hidima ba wai su ne za su mun hidima ba. Zan yi aiki tamkar bawansu."

A wace jam'iyyar malamin cocin zai yi takara?

Sai dai Obinyan bai bayyana wace jam'iyyar siyasa zai shiga domin cimma burinsa na zama gwamnan jihar Edo ba.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Manyan malamai sun dira hedkwatar tsaro ta kasa yayin da CDS ya dauki sabon alkawari

Amma ya ƙara da bayanin cewa a shirye yake a kowane lokaci domin yi wa al'umma hidima, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Hukumar zaɓe ta kasa mai zaman kanta (INEC) za ta gudanar da zaɓen gwamnan Edo a watan Satumba na shekarar 2024.

Tinubu Ya Sansanta Ricikin Minista da Gwamnan PDP

A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya warware rikicin siyasar da ya shiga tsakanin Gwamna Fubara na Ribas da ministan Abuja, Nyesom Wike

A taron neman maslaha da ya gudana a Villa, Wike da Gwamna Fubara sun rattaba hannu kan yarjejeniya guda takwas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel