A Karshe, Shugaba Tinubu Ya Sansanta Ricikin Minista da Gwamnan PDP Kan Sharuɗda 8
- Bola Ahmed Tinubu ya warware rikicin siyasar da ya shiga tsakanin Gwamna Fubara na Ribas da ministan Abuja, Nyesom Wike
- A taron neman maslaha da ya gudana a Villa, Wike da Gwamna Fubara sun rattaba hannu kan yarjejeniya mai kunshe da abu takwas
- Gwamna Fubara da uban gidansa a siyasa sun samu saɓani ne tun lokacin da majalisar dokokin Ribas ta yi yunkurin tsige shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - A karshe, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya samu nasarar lalubo bakin zaren da zai kawo karshen dambarwar siyasar da ta ɓarke a jihar Ribas.
Yayin zaman sulhu da masu ruwa da tsakin jihar Ribas, Bola Tinubu ya kama hanyar warware saɓanin da ya shiga tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da ministan Abuja, Nyesom Wike.
A wata sanarwa da hadimin shugaban ƙasa ya wallafa a Twitter, Tinubu ya yi taron sirri da Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas, Peter Odili da wasu jiga-jigai domin warware matsalar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Fubara, wanda ya halarci zaman a fadar shugaban ƙasa, ya rattaba hannu kan yarjejeniya tare da yan majalisar dokokin jihar da suka sauya sheƙa zuwa APC.
Fubara zai janye kararrakin da ya shigar kotu
Gwamnan ya kuma amince zai janye dukkan kararrakin da ya shigar gaban kotu kan ƴan majalisar masu goyon bayan Wike da suka sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.
Haka nan kuma majalisar dokokin jihar Ribas ta amince zata dakatar da duk wani yunƙuri na tsige Gwamna daga kan madafun iko.
Ƙarin wata matsayar da aka cimmawa a taron sasancin ita ce barin ɓangaren majalisa su yi aikinsu ba tare da yi masu katsalandan ba.
Tsagin Wike da tsagin Fubara duk sun aminta cewa gwamnan ba zai sake tsoma baki kan harkonin majalisa ba yayin da su kuma ƴan majalisar za a basu daman yin zamansu duk suke so.
Fubara ya kuma yarda cewa zai sakar wa majalisar dukkan kuɗaɗenta kuna ba zai tsoma baki kan yadda majalisar zata kashe kuɗin ba.
Shugaba Bola Tinubu Ya Sa Labule da Wakilan NPAN
A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu na ganawa da wakilan kungiyar gidajen jaridu ta ƙasa (NPAN) a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja.
Shugaban kamfanin jaridar Daily Trust kuma shugaban NPAN na ƙasa, Malam Kabiru Yusuf, ne ya jagoranci tawagar zuwa Villa.
Asali: Legit.ng