Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Ƴan Majalisar Tarayya 4 a Arewa, PDP Ta Yi Martani

Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Ƴan Majalisar Tarayya 4 a Arewa, PDP Ta Yi Martani

  • Jam'iyyar PDP a jihar Sakkwato ta mayar da martani kan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara game da zaben yan majalisar wakilai huɗu
  • A wata sanarwa, PDP ta nuna farin ciki bisa yadda ƴan takararta suka samu nasara, tana mai cewa abinda mutane suka zaɓa ne ya tabbata
  • Ta kuma roƙi ɗaukacin al'ummar jihar su ci gaba da mara mata baya domin samun jagoranci na gari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Sokoto - Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Sakkwato ta nuna gamsuwa da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara kan nasarar ƴan majalisar wakilai huɗu na jihar.

Jam'iyyar PDP ta bayyana jin daɗinta da hukuncin a wata sanarwa da mai magana da yawun jam'iyyar na jihar Sakkwato, Hassan Sayinnawal, ya fitar ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Gwamna Fintiri ya aike da sako mai muhimmanci yayin da kotun kara za ta yanke hukunci

Jam'iyyar PDP ta ji daɗin hukuncin kotun ɗaukaka ƙara.
Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar yan majalisar tarayya 4, PDP ta yi murna Hoto: OfficialPDPNigeria
Asali: Twitter

Mambobin majalisar wakilai huɗu na PDP da suka samu nasara a kotun ɗaukaka ƙarar sun haɗa da Mani Katami, mai wakilatar Binji/Silame da Abdussamad Dasuki mai wakiltar Kebbe/Tambuwal.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun haɗa da, mamba mai wakiltar mazaɓar Sabon Birni/Isa, Sa’idu Bargaja da takwaransa mai wakiltar mazaɓar Goronyo Gada, Bashir Gorau, kamar yadda Punch ta ruwaito.

PDP ta maida martani

A sanarwan, kakakin PDP na Sokoto ya ce:

"Jam'iyyar PDP a jihar Sokoto tayi farin ciki dangane da nasarar da 'yan majalisar tarayya na jam'iyyar suka samu game da zaben 2023 a kotun daukaka kara ta Najeriya."
"PDP na ganin wannan nasara na nuna yadda al'umma ke da kwarin guiwa ga ƴan takarar da jam'iyyar da tsayar da kuma muradinsu na samun jagoranci na gari."
"Jam’iyyarmu tana kira ga jama’a da su ci gaba da ba da goyon bayansu ga kyawawan manufofinmu da kuma kwarin gwiwar cewa zaɓinsu na 2023 zai tabbata a kowace shari'a."

Kara karanta wannan

Dalibai mata na jami'ar arewa sun kuɓuta daga hannun yan bindiga, VC ya faɗi halin da suke ciki

Yadda kotun ɗaukaka ƙara ta yi hukunci

Kotun ɗaukaka ƙara ta ayyana Mani Katami na PDP a matsayin sahihin wanda ya ci zaɓe a mazaɓar Binji/Silame, wanda zai maye gurbin ɗan takarar APC da INEC ta ba nasara a farko.

Ranar Asabar kuma kotun ta tabbatar da nasarar Abdulsamad Dasuki da Bashir Gorau, duk na PDP, a zaɓen da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu, Tribune ta rahoto.

CDS ya sha alwashin fallasa masu laifi

A wani rahoton kuma CDS Christopher Musa ya sha alwashin tona asirin duk wanda ya gano da hannu a harƙallar miyagun kwayoyi a Najeriya.

Babban hafsan tsaron ya ɗauki wannan alƙawarin ne yayin ganawa da shugaban NDLEA na ƙasa, Buba Marwa a Abuja ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262