Wanda ya kafa NNPP, Aniebonam, ya shirya addu'o'i na musamman saboda gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

Wanda ya kafa NNPP, Aniebonam, ya shirya addu'o'i na musamman saboda gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

  • Dakta Boniface Aniebonam, wanda ya kafa jam'iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ya shirya addu'a ta musamman domin nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf a Kotun Koli
  • Aniebonam, har ila yau ya yi magana kan rikicin da ake rahotowa na faruwa a NNPP inda ya ce babu wata rikici kuma babu rashin jituwa tsakaninsa da Rabiu Musa Kwankwaso
  • Kwamitin Gudanarwa na jam'iyyar NNPP wato NWC wacce ke biyayya ga jagoran jam'iyyar na kasa Rabiu Musa Kwankwaso ta dakatar da Dakta Boniface Aniebonam

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Wanda ya kafa jam'iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Dr. Boniface Aniebonam, a jiya Alhamis ya jagoranci kungiyarsa, 'National Association of Government Approved Freight Forwarders (NAGAFF)' don shirya addu'a na musamman ga Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, don neman sa'a daga Allah gabanin hukuncin Kotun Koli dangane da karar da suka daukaka.

Kara karanta wannan

Bayanai sun fito kan haduwar Kwankwaso da jagororin NNPP kafin zaman kotun koli

Gwamna Abba Kabir Yusuf
Dr Aniebonam ya shirya addu'a na musamman don nasarar Abba Gida-Gida a Kotun Koli. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Kwamitin Gudanarwa na Jam'iyyar (NWC) wacce ke biyayya ga dan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso ta dakatar da Aniebonam, wanda shine ya kafa NAGAFF kuma shugaban kwamitin amintattu na NNPP.

Babu matsala tsakanina da Kwankwaso, Aniebonam

Amma da ya ke magana wurin taron addu'an, Aniebonam ya ce babu matsala a NNPP tunda shi da Kwankwaso ba su yi wani takamammen magana ba kan rikicin jam'iyyar da ake ta yadawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce bisa tsarin kundin tsarin mulkin kasa da doka, har yanzu Yusuf ne jagoran jam'iyyar a Kano.

A cewarsa:

"Ina magana da Gwamna Abba Yusuf hakan ne dalilin da yasa na kira wannan taron addu'o'in. Ina son cewa babu wata matsala tsakanina da Kwankwaso."
Ya bayyana abin da ke faruwa a jam'iyyar a matsayin "muryan yara saboda abin da za su saka a cikinsu."

Kara karanta wannan

Rikicin siyasar Rivers: Jigon APC ya yi wa Gwamna Fubara wankin babban bargo

Idan za a iya tunawa Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja ta jadada hukuncin Kotun Sauraron Karar Gwamnan Jihar Kano wacce ta soke zaben Yusuf, gwamnan NNPP tilo a kasar, rahoton NAN.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164