Kujerun Ciyamomi 31 Sun Fara Tangal-Tangal a Ranar da Gwamnan PDP Ya Rantsar da Su
- Gwamna Umo Eno ya rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi 31 da ke faɗin jihar Akwa Ibom ranar Alhamis
- Da yake jawabi a wurin bikin rantsuwar kama aiki, Gwamnan ya ce zai kori duk wanda ya ƙauracewa zama a yankinsa
- Ya ce dole kowane ciyaman ko babban jami'in ƙaramar hukuma ya zauna tare da al'ummar da yake jagoranta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Akwa Ibom - Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya sha alwashin korar duk wani shugaban karamar hukumar da ya daina zama a yankinsa.
Gwamna Eno ya bayyana haka ne ranar Alhamis a gidan gwamnati da ke Uyo, yayin bikin rantsar da gwamnatin rikon kwarya ta kananan hukumomi 31 na jihar.
Atiku da Ɗangote sun lale Naira biliyan uku sun baiwa ɗan takarar gwamna a arewa? Gaskiya ta yi halinta
Majalisar dokokin jihar Akwa Ibom ta amince da bukatar gwamnan ta naɗa gwamnatin riƙon kwarya a kananan hukumomin biyo bayan ƙarewar wa'adin zababbun ciyamomi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Premium Times ta tattaro cewa wa'adin zababbun shugabannin kananan hukumomin ya ƙare ne da daren ranar Laraba, 6 ga watan Disamba.
Gwamna ya rantsar da kantomomi
Da yake jawabi jim kaɗan bayan shaida rantsuwar kama aikin waɗanda zasu jagoranci ƙananan hukumomin, Gwamna Eno ya jaddada matsayarsa cewa dole su zauma a yankunansu.
Tun da farko gwamnan ya aike da kudiri ga majalisar dokokin jihar domin tilastawa manyan jami'an kananan hukumomin su zauna a yankinsu amma daga baya ya janye.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya janye kudirin ne bayan ya fahimci cewa tun asali daman akwai dokar amma ba a aiki da ita.
A jawabin da ya yi wa shugabannin kananan hukumomin, Gwamna Eno ya ce:
"Ina kara jaddada muku cewa dole ku zauna a kananan hukumominku, ba zai yiwu ku shugabanci yankunanku daga wani wuri ba."
"Idan na gano wani na zaune a birnin Uyo kuma yana mulkin wata ƙaramar hukuma, zan tattara bayanan sirri, sannan na sanar da cewa na tsige shi ko waye."
"Ku koma gida ku zaune tare da mutanen ku ta yadda zaku sake farfaɗo da ayyukan kananan hukumomi. Duk wanda ya san ba zai zauna a yankinsa ba zai iya yin murabus."
Kwankwaso Ya Shirya Haɗewa da Shugaba Tinubu da APC
A wani rahoton kuma Abdulmumini Kofa ya musanta rahoton da ke cewa NNPP ta fara tattaunawar haɗa maja da PDP da wasu jam'iyyun adawa.
Ɗan majalisar tarayya ya jaddada cewa kofar NNPP a buɗe take ta yi aiki da kowa amma a yanzu babu wata tattaunawa da aka fara.
Asali: Legit.ng