Kwamishina Ya Fadi Gaskiya, Ya Tona Asirin Jiga-Jigan Gwamnati da ke Jabun Sa Hannun Gwamnan APC
- Alamu sun ƙara tabbatar da cewa wasu muƙarraban gwamnatin Ondo suna yin jabun sa hannun Gwamna Rotimi Akeredolu
- Kwamishinan makamashi, Razaq Obe, ya tabbatar da haka a wata wasiƙa da ya aike wa mataimakin gwamna, Lucky Ayedatiwa
- Ya ce bayan mayar da wani fayil zuwa ma'aikatarsa, ya tura wa kwararru kuma sun tantance sa hannun gaskiya da na jabu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Rikicin siyasar jihar Ondo ya buɗe sabon shafi yayin da zargin da ake na wasu muƙarraban gwamnatin jihar na jabun sa hannun gwamna ya fara fitowa daga bakin kwamishinoni.
Kwamishinan makamashi da ma'adanan ƙasa na jihar Ondo, Razaq Obe, ya tabbatar da cewa wasu shafaffu da mai na yin jabun sa hannun Gwamna Rotimi Akeredolu.
Ya yi wannan furuci ne kwanaki kalilan bayan wani babban lauya, Kayode Ajulo, SAN, ya fallasa cewa wasu kwamishinoni sun fara jabun sa hannun gwamnan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Jumu'a 8 ga watan Disamba, Mista Obi ya bayyana cewa an kwaikwayi sa hannun gwamnan a wata takarda, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Kwamishinan ya tabbatar da haka ne a wata wasiƙa da ya aike wa mataimakin gwamnan jihar, Lucky Ayedatiwa.
'Yadda muka tantance jabun sa hannun gwamna'
Ya ce an gano kura-kuran jabun sa hannun ne a cikin wata takarda da aka mayar wa ma’aikatarsa ta hannun ofishin sakataren gwamnatin jihar (SSG).
Ya bayyana cewa ya aika takardar ga kwararrun masu bincike don tabbatar da sahihanci, kuma sun tabbatar da cewa sa hannun da ke jiki da rubutun hannu na jabu ne.
A rahoton The Nation, Wasiƙar kwamishinan ta ce:
"Na rubuta wannan wasiƙa ne domin na ja hankalinka kan wani muhimmin batu da yake bukatar ɗaukar matakin gaggawa. Ta tabbata an yi sa hannun mai girma gwamna na jabu."
"Mun fahimci haka ne yayin da aka dawo da wani fayil ga ma'aikatar da nake jagoranta daga ofishin sakataren gwamnati, shi ne na farko da ya dawo daga cikin guda biyar da muka tura domin neman izinin gwamna."
"Bayan na duba sosai, na lura akwai banbanci tsakanin sa hannun da ake tuhuma da rubutun hannun gwamna da ke a cikin fayil ɗin. "
"Ina rokon ka gaggauta duba zuwa wannan batu kuma ka ɗauki matakin cikin hanzari," in ji kwamishinan.
Melaye ya faɗi gaskiya kan zargin laƙume N3bn
A wani rahoton kuma Sanata Dino Melaye ya musanta jita-jitar cewa Atiku da Ɗangote sun ba shi N3bn kafin zaben gwamnan jihar Kogi.
Melaye, ɗan takarar PDP a zaben da aka yi ranar 11 ga watan Nuwamba, ya ce rahoton kanzon kurege ne babu kanshin gaskiya.
Asali: Legit.ng