Hotuna: Magoya Bayan NNPP da Abba Sun Gamu da Babbar Matsala Yayin da Suka Fito Taro a Kano

Hotuna: Magoya Bayan NNPP da Abba Sun Gamu da Babbar Matsala Yayin da Suka Fito Taro a Kano

  • Magoya bayan NNPP da Gwamna Abba Kabir Yusuf sun gamu da cikas yayin da suka fito taron addu'ar neman nasara ranar Alhamis
  • Jami'an yan sanda da sibil defens sun hana mambobin jam'iyyar shiga filin da suka shirya taron, bisa dole suka koma gefe ɗaya
  • Kakakin hukumar sibil defens ya bayyana cewa an yi haka ne domin tabbatar da babu wanda ya taka doka da oda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Kano - Dakarun yan sanda da haɗin guiwa jami'an sibil defens sun hana magoya bayan jam'iyyar NNPP su yi taron addu'o'i a cikin birnin Kano.

Magoya bayan NNPP sun gamu da cikas.
Jami'an tsaro sun hana magoya bayan NNPP gudanar da taron addu'a a Kano Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Daily Trust ta ce rigima ta ɓalle tsakanin mambobin NNPP da yan sanda yayin da suka fito wurin taron addu'a makamancin wannan jiya Laraba da yamma.

Idan baku manta ba, magoya bayan NNPP sun fantsama zanga-zanga kan tituna domin nuna fushi kan ruɗanin da aka samu a takardun hukunci tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

Tsige Abba: Tashin hankali yayin da APC da NNPP suka shirya gagarumin abu rana ɗaya a Kano

Duk da alkalan Kotun ɗaukaka ƙara sun tsige Gwamnan Kano, wani feji a cikin kundin hukuncin (CTC) ya tabbatar da nasarar Abba Gida-Gida, Premium Times ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan sanda sun hana ƴan NNPP taro yau Alhamis

Amma a ranar Alhamis, 23 ga watan Nuwamba, 2023, magoya bayan NNPP sun ga ikon Allah yayin da aka hana su shiga filin Marhala, wurin da suka tsara taron addu'o'in neman nasara.

Maimakon su bar wurin gaba ɗaya, mambobin NNPP sun koma ɗaya ɓangaren Filin Na'isa, suka tsaya cirko-cirko suna kallon jami'an tsaron.

Duk wani yunƙurin jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na hukumar yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, kan abin da ya faru bai kai ga nasara ba.

Sai dai jami’in hulda da jama’a na hukumar NSCDC, DSC Idris Abdullahi, ya ce an tura jami’an ne domin tabbatar da bin doka da oda a jihar.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: An bankaɗo sabbon shirin NNPP kan wasu kusoshin APC a Kano bayan tsige Abba

Ya ce:

"Mun yi haka ne duba da abin ke faruwa sakamakon hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da sauran batutuwa masu alaƙa da shi. Bisa haka aka ƙara girke dakaru don tabbatar da doka."

Hotunan yadda abun ya faru

Yadda aka hana NNPP taro a Kano.
Jami'an tsaro sun hana magoya bayan NNPP gudanar da taron addu'a a Kano Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Yadda aka hana NNPP taro a Kano.
Jami'an tsaro sun hana magoya bayan NNPP gudanar da taron addu'a a Kano Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Mamban NNPP da ya halarci wurin, Abubakar Mahmud, ya shaida wa Legit Hausa cewa sun je taron addu'a amma ƙiri-kiri jami'an tsaro suka hana su shiga.

A kalamansa ya ce:

"Ni ne na ja Sallah a wurin, da farko da muka je da misalin ƙarfe 9:30 na safe, kwatsam sai ga yan sanda a motoci suka hana mu shiga, na taƙaice maka har da duka."
"Daga bisani muka yi maslaha muka yi sallar mu a gefen titi ba tare da mun tada yamutsi ba, muka haɗa sahu muka yi sallah muka yi addu'a, yan sandan ba su ce mana komai ba har muka gama muka watse."

Kotun ɗaukaka kara ta kori ɗan majalisa

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai sabon kazamin hari a arewa, sun tafka ɓarna mai muni tare da kashe bayin Allah

A wani rahoton kuma Kotun ɗaukaka ƙara ta kori ɗan majalisar PDP, ta ayyana APC a matsayin wacce ta samu nasara a zaben mamban majalisar dokokin Ogun.

Kotun ta bayyana cewa ta gamsu da hujjojin cewa ɗan takarar PDP, Owodunni ya janye daga takara a mazabar mamba mai wakiltar Ikenne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262