Ana Tsaka da Ruɗani Kan Tsige Abba Gida-Gida, Ganduje Ya Kori Wasu Shugabannin APC Na Jiha Guda
- Jam'iyyar APC ta ƙasa ta kori dukkan shugabanninta na jihar Ribas ta naɗa sabon kwamitin rikon kwarya
- Jam'iyyar ta cimma wannan matsaya ne a wurin taron kwamitin gudanarwa NWC na ƙasa karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Ganduje
- Kakakin APC na ƙasa, Felix Morka ya bayyana cewa za a rantsar da kwamitin rikon ranar Jumu'a mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar APC ta ƙasa (NWC) ya tsige baki ɗaya shugabannin jam'iyyar na jihar Ribas.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jam'iyyar APC ta wallafa a shafinta na manhajar X wadda aka fi sani da Tuwita ranar Laraba.
Jam'iyyar APC ta naɗa kwamitin rikon kwarya
NWC na kasa karƙashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kuma naɗa kwamitin rikon kwarya da zai jagorancu shirya gangamin zaɓen shugabannun APC a Ribas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi ga ƴan jarida a Abuja ranar Laraba, Sakataren watsa labaran APC na ƙasa, Felix Morka, ya ce ranar Jumu'a za a kaddamar da kwamitin riƙon kwarya.
Morka, wanda ke tare da mataimakisa na APC, Duro Ladipo, ya karanto sunayen magoya bayan ministan Abuja, Nyesom Wike a matsayin mambobin kwamitin wanda ya ƙunshi mutum bakwai.
Kakakin APC ya ce:
"Mun yanke shawarar rushe shugabancin APC na jihar Ribas a taron NWC kuma mun amince da naɗa kwamitin rikon kwarya a jihar."
"Kwamitin ya ƙunshi Chief Tony Okocha a matsayin shugaba da kuma Eric Nwibani a matsayin sakatare. Sauran mambobin su ne Chibuike Ikenga, Stephen Abolo, Silvester Vidin, Senibo Dan-Jumbo da Mis Darling Amadi."
"Ranar Jumu'a mai zuwa za a rantsar da kwamitin rikon kwaryan a nan sakatariyar APC ta ƙasa."
Morka ya kuma ce kwamitin riko zai shafe tsawon watanni shida har sai an zabi wasu shugabannin jam'iyyar APC reshen jihar Ribas.
Fadar shugaban kasa ta yi magana kan lafiyar Tinubu
A wani rahoton na daban Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa lafiyar Shugaba Tinubu kalau ba abinda ke damunsa in banda kafar da aka masa tiyata
Mai ba shugaban kasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya ce tun tiyatar da aka yi wa Tinubu a guiwa a 2021 har yau yana jinya
Asali: Legit.ng