Tsohon Minista Na PDP Ya Zama Sabon Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Dattawa
- Sanata Abba Moro na PDP daga jihar Benuwai ya zama sabon shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawan Najeriya
- Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ne ya sanar da naɗin tsohon ministan, wanda zai maye gurbin Sanatan Filato da kotu ta tsige
- An ce hatsaniya ta ɓalle a zauren majalisar bayan sanar da sabon mai ladabtarwa na marasa rinjaye a majalisar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da.kullum
FCT Abuja - Tsohon ministan harkokin cikin gida kuma Sanata a karo na huɗu a inuwar PDP, Sanata Abba Moro, ya zama sabon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa.
Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio ne ya sanar da naɗin a zauren majalisar dattawa da ke Abuja ranar Talata, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Jaridar Punch ta tattaro cewa mambobin majalisar dattawa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun amince su miƙa kujerar ga shiyyar Arewa ta Tsakiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatocin babbar jam'iyyar adawan sun ɗauki wannan matakin ne domin a samu adalci da daidaito a tsarin raba muƙaman majalisar dattawa ta 10.
Legit Hausa ta fahimci cewa Sanata Abba Moro ya fito ne daga jihar Benuwai, ɗaya daga cikin jihohin shiyyar Arewa ta Tsakiya a Najeriya.
Ya maye gurbin Sanata Simon Nwadkwon mai wakiltar Filato ta Arewa a karkashin jam’iyyar PDP wanda kotu ta kora a ranar 23 ga watan Oktoba.
Hayaniya ta ɓarke bayan sanar da sabon mai ladabtarwa
Sai dai hatsaniya ta ɓalle a zauren majalisar dattawa bayan sanar da naɗin Sanata Osita Ngwu (Enugu ta yamma, PDP) a matsayin sabon mai ladabtarwa na marasa rinjaye.
Sabon mai ladabtarwan aka naɗa sai maye gurbin Sanata Darlington Nwokwocha na Labour Party.
Sanata Okechukwu Ezea daga mazaɓar Enugu ta Arewa ya tashi ya caccaki sabon nadin kuma Sanata Tony Nwoye na LP ya goyi bayansa nan take.
Ya kalubalanci matakin miƙa wa PDP gaba ɗaya jagorancin marasa rinjaye, wanda hakan ya bar jam'iyyar LP kwanko, ba ta da wakili a jagorancin majalisar dattawa.
Bayan hatsaniya mai zafi, shugaban majalisar ya dauki mafi rinjaye bayan kaɗa kuri'ar amincewa PDP ta karɓi muƙamin.
Buhari ya faɗi manufar canza kuɗi
A wani rahoton na daban Muhammadu Buhari ya bayyana muhimmin dalilin da ya sa gwamnatinsa ta canza fasalin Naira ana dab da zaɓen 2023.
Tsohon shugaban kasan ya ce ya yi haka ne domin nuna wa yan Najeriya cewa babu hanyar samun mulki cikin sauƙi.
Asali: Legit.ng