Jigon PDP Kuma Lauya Ya Feɗe Gaskiya Kan Hukuncin Kotun Ɗaukaka Kara Na Tsige Gwamnan Arewa

Jigon PDP Kuma Lauya Ya Feɗe Gaskiya Kan Hukuncin Kotun Ɗaukaka Kara Na Tsige Gwamnan Arewa

  • Jigon PDP, Daniel Bwala ya caccaki matakin tsige gwamnan jihar Filato da Kotun ɗaukaka ƙara ta yi ranar Lahadi
  • A wata hira, tsohon kakakin kwamitin kamfen shugaban ƙasa na PDP ya ce ba a taɓa soke zaɓe saboda wani ya ƙi bin umarnin kotu ba
  • Ya ce zasu jira su ga hukuncin da kotu zata yanke kan zaben gwamnan jihar Ebonyi domin matsala ɗaya ce da ta PDP a Filato

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Babban jigo a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Daniel Bwala, ya soki hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na tsige Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato.

Babban jigo a PDP, Daniel Bwala.
Bwala Ya Caccaki Hukuncin Kotun Daukaka Kara Na Tsige Gwamnan Filato Hoto: Channelstv
Asali: UGC

Mista Bwala ya bayyana cewa ko kaɗan bai taɓa ganin inda aka soke inganci zaɓe saboda wani ya kaucewa umarnin Kotu ba.

Kara karanta wannan

"INEC Ce" Tsohon kakakin kwamitin kamfen Atiku ya gano babbar matsalar da aka samu a zaben 2023

Jigon kuma tsohon mai magana da yawun kwamitin kamfen shugaban ƙasa na PDP ya yi wannan furucin ne a wata hira da Channels tv cikin shirin siyasa a yau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ba mu taba ganin inda aka soke zabe ba saboda wani ya ki bin umarnin kotu," in ji shi.

Tun farko, hukumar zaɓe ta ayyana Gwamna Mutfwang a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Filato wanda aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023.

A cewar INEC, gwamnan, ɗan takarar a inuwar PDP ya samu ƙuri'u 525,299 wanda ya ba shi damar lallasa a abokan karawarsa 17 ciki harda ɗan takarar APC, Nentawe Goshwe mai ƙuri'u 481,370.

A watan Satumba, Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben gwamnan Filato ta tabbatar da nasarar Gwamna Mutfwang na PDP, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jigon NNPP ya dora alhakin tsige Gwamna Abba Kabir kan Kwankwaso, ya bayyana dalilansa

Amma watanni biyu bayan haka ranar Lahadin da ta gabata, kotun ɗaukaka ƙara ta tsige gwamnan kuma ta umarci INEC ta bai wa ɗan takarar APC shaidar lashe zabe.

Babu dalilin tsige gwamnan Filato - Bwala

Da yake martani kan hukuncin, Bwala, wanda lauya ne masanin doka, ya ce bai kamata a soke sahihancin zaɓen ba saboda umarnin kotu kan tarukan jam'iyar PDP.

Ya ce:

"Idan ka duba sashi na 134, babu rashin bin umarnin kotu a wurin. Yanzu kotu na iya cewa rashin bin umarnin ne ya shafi gudanar da zaɓen fidda gwani."
"Kuma ko da a ce ba su gudanar da zaɓen fidda gwani ba, duk al'amura ne na kafin zaɓe, ina ganin ya fi muhimmanci fiye da ƙin bin umarnin kotu."

Ya kuma yi kira ga mazauna jihar Filato su kwantar da hankalinsu domin a yanzu sun zura ido su ga hukuncin da za a yanke kan zaɓen jihar Ebonyi, wanda ke da matsala iri ɗaya.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Babban malamin addini ya yi magana kan yiwuwar tsige Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa

Shin Tinubu na da hannu a tsige gwamnonin adawa?

A wani rahoton kuma Fadar shugaban ƙasa ta maida martani kan kalamam Atiku Abubakar da PDP dangane da gwamnonin da Kotun ɗaukaka ƙara ta tsige.

A wata sanarwa da Bayo Onanuga ya fitar ranar Litinin, ta ce Shugaba Tinubu ba ya tsoma baki a harkokin ɓangaren shari'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262