Jigon NNPP Ya Yi Zazzafan Martani Kan Hukuncin Kotun Daukaka Kara Na Sauke Abba Gida-Gida

Jigon NNPP Ya Yi Zazzafan Martani Kan Hukuncin Kotun Daukaka Kara Na Sauke Abba Gida-Gida

  • Kotun daukaka kara ta soke zaben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a Abuja a ranar Juma'a, 17 ga watan Nuwamba
  • Kotun daukaka karar ta riki cewa Yusuf, dan takarar NNPP, a zaben na watan Maris a jihar Kano, ban cancanci yin takara ba
  • Hukuncin kotun ya haddasa cece-kuce, kuma wani jigon NNPP, Razaq Aderibigbe, ya zanta da jaridar Legit

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Kano, jihar Kano - Adekunle Razaq Aderibigbe, jigon jam'iyyar NNPP a jihar Lagas, ya bayyana hukuncin kotun daukaka kara da ta tsige Gwamna Abba Yusuf a ranar Juma'a, 17 ga watan Nuwamba, a matsayin "wani yunkuri na yiwa masu rinjaye fashi".

Da yake zantawa da jaridar Legit a wata hira da shi a ranar Asabar, 18 ga watan Nuwamba, Aderibigbe ya fusata da hukuncin kotun.

Kara karanta wannan

Hukuncin kotun daukaka kara: Farfesan arewa ya yi gargadi kan yiwuwar barkewar rikici a Kano

Jigon NNPP ya yi watsi da tsige Abba da kotun daukaka kara ta yi
Kano: “Hukunci Kotun Daukaka Kara, Yunkuri Ne Na Yiwa Masu Rinjaye Fashi”, Jigon NNPP Hoto: @qunley, @Gawuna2023, @Kyusufabba
Asali: Twitter

'Kin yi kuskuren dasa ayar tambaya kan kasancewar Yusuf dan jam'iyya', Aderibigbe ga kotu

Tsohon dan takarar na kujerar majalisar dokokin jihar Legas ya bayyana cewa hukuncin kwamitin da mai shari’a M. U. Adumeh ya jagoranta ya yanke abin dariya ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana kan al’amuran siyasa a Kano, Aderibigbe ya ce:

"Hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na soke zaben gwamnan jihar Kano ba wai kawai mayar da tsarin dimokradiyya abun dariya ya yi ba har ma da mahimmancin rawar ganin yan kasa a babban zabe.
“Gwamna Abba Kabir Yusuf bai taba samun matsala da kowani dan NNPP a matsayin dan jam’iyyar ba har zuwa lokacin da aka zabe shi, haka kuma hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) bata hana shi zama dan jam'iyya ba. Kalubalantar kasancewarsa dan jam'iyya a wannan lokaci, watanni takwas bayan zabe ba hujja bace na soke sakamakon zaben bayan INEC ta gudanar da aiki da zabin kanawa miliyan 1.

Kara karanta wannan

"Yan maula sun fara": Jama’a sun yi caaa kan Ali Nuhu bayan ya taya Gawuna murnar nasara a kotun

“Ba yadda za a yi ace jam’iyyar NNPP ba za ta yi amfani da yancin jin ta bakinta da neman adalci ba ta hanyar kalubalantar hukuncin a kotun koli da fatan cewa doka za ta maido da nasara ga mai ita da muradun mafi rinjayen Kanawa miliyan 1 da suka zabi Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ga hukuncin ganin dama da aka yanke."

Kperogi ya yi gargadi kan tsige Abba

A wani labarin, mun ji cewa Farfesa Farooq Kperogi, haifaffen dan jihar Kwara mazaunin Amurka, ya soki hukuncin kotun daukaka kara da ya tabbatar da tsige Gwamna Abba Yusuf.

Kperogi, a cikin wallafarsa a ranar Asabar, 18 ga Nuwamba, ya ce "yana fatan wannan cin zarafi da aka yi kan gaskiya ba shine tartsatsin da zai kunna wutar rikici ba a Kano - da kasar."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng