Gwamnan Arewa Ya Maida Martani Kan Hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Yanke
- Gwamnan Bauchi, Bala Muhammed, ya maida martani bayan Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan nasarar da ya samu
- Kauran Bauchi ya yaba da hukuncin wanda ya ƙara tabbatar da sahihancin zaɓen da ya lashe ranar 18 ga watan Maris
- Ya kuma yi kira ga jam'iyyun adawa su haɗu wuri ɗaya su mara masa baya wajen gina sabuwar jihar Bauchi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammed, ya yaba da hukuncin Kotun ɗaukaka wanda ya tabbatar da nasarar da ya samu a zaɓen gwamna.
Gwamnan ya faɗi haka ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na manhajar X wadda aka fi sani da Twitter ranar Jumu'a, 17 ga watan Nuwamba, 2023.
Yayin da take yanke hukunci, Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta tabbatar da nasarar Ƙauran Bauchi a zaɓen da aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake martani bayan samun nasara, Gwamna Muhammed ya bayyana nasarar da ya samu a matsayin, "shaida ga sadaukarwan da yake wajen shayar da mutane romon Demokuraɗiyya."
Kauran Bauchi ya aike da sako ga ƴan adawa
A sakon da ya wallafa a shafinsa, gwamnan ya ce:
"Bisa haka ina kira ga dukkan jam'iyyun adawa a nan cikin jiharmu su dunƙule wuri ɗaya su goyi bayan kudirin gina sabuwar Bauchi wanda zai maida hankali wajen kawo sauyi na gari."
"Ina ƙara miƙa godiya ga shugabancin jam'iyyar PDP reshen jihar Bauchi, dumbin magoya bayanmu masu albarka da ɗaukacin al'umma bisa goyon bayan da suke bamu da addu'a."
"Wannan nasara taku ce kamar yadda take tawa, kuma na yi alƙawarin amfani da wannan nasarar wajen gina kwakkyawan jagoranci wanda kuke muradin samu."
A cewar gwamnan, "mu haɗa kai mu bude sabon babi a Jihar Bauchi, mai ƙunshe da ci gaba, hadin kai, da wadata.”
Jami'an Tsaro Sun Ɗauki Mataki a Wasu Wurare a Kano
A wani rahoton na daban kuma An girke jami'an tsaro a muhimman wurare domin tabbatar da doka da oda a cikin kwaryar birnin Kano bayan hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara.
Wannan na zuwa ne bayan tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP daga matsayin gwamnan jihar Kano ranar Jumu'a.
Asali: Legit.ng