SDP Ta Lallasa APC da PDP a Kananan Hukumomi 5 Yayin da Ake Tattara Sakamakon Zaben Gwamnan Kogi
Jihar Kogi, Lokoja - Muritala Ajaka, dan takarar jam'iyyar SDP a zaben gwamnan jihar Kogi da aka yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, ya yi gagarumin nasara a kananan hukumomi biyar (5).
Koda dai hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta fara tattara sakamakon karshe a jihar, amma dai hukumar bata riga ta sanar da wanda ya lashe zaben ba a ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba.
Sai dai kuma, sakamakon zaben da aka tattara daga shafin IRev na INEC zuwa yanzu, ya nuna Usman Ododo na jam'iyyar APC da Ajaka na SDP sun yi wa dan takarar PDP, Sanata Dino Melaye zarra.
Ga daki-daki na sakamakon zaben da aka tattara a kanan hukumomi biyar inda Ajaka ya yi nasara:
Sakamakon da The Cable ta tattara ya zo kamar haka:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Karamar hukumar Olamaboro , Kogi
Murtala Ajaka, dan takarar gwamnan SDP ya yi nasara a kananan hukumomi biyar.
Masu rijista: 105,864
Masu zabe da aka tantance: 30,287
ADC: 126
APC: 5,572
PDP: 1,376
SDP: 22,173
Kuri'u masu inganci: 29,731
Lalatattun kuri'u: 495
Jimillar kuri'u da aka kada: 30,226
2. Karamar hukumar Omala, Kogi
Masu rijista: 74,537
Masu zabe da aka tantance: 22,538
ADC: 218
APC: 2,902
PDP: 832
SDP: 18,160
Kuri'u masu inganci: 22,317
Lalatattun kuri'u: 196
Jimillar kuri'u da aka kada: 22,51
3. Karamar hukumar Ofu, Kogi
Masu rijista: 101,964
Masu zabe da aka tantance: 36,087
ADC: 297
APC: 5,245
PDP: 293
SDP: 28,768
Kuri'u masu inganci: 35,180
Lalatattun kuri'u: 587
Jimillar kuri'u da aka kada: 35,767
4. Karamar hukumar Idah, Kogi
Murtala Akaja, dan takarar SDP, ya lashe fiye da kaso 80 na kuri'u a karamar hukumarsa
Masu rijista: 64,339
Masu zabe da aka tantance: 23,044
APC: 2,033
PDP: 271
SDP: 20,059
Kuri'u masu inganci: 22,742
Lalatattun kuri'u: 280
Jimillar kuri'u da aka kada: 23,022
5. Karamar hukumar Ankpa, Kogi
Masu rijista: 180,095
Masu zabe da aka tantance: 57,650
ADC: 186
APC: 8,707
PDP: 3,654 SDP: 43,258
Kuri'u masu inganci: 56,395
Lalatattun kuri'u: 873
Jimillar kuri'u da aka kada: 57,268
Asali: Legit.ng