Zaben Gwamnan Bayelsa: An Sanar Da Wanda Ya Lashe Zabe A Rumfar Zaben Gwamna Diri
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Yenagoa, Jihar Bayelsa - Douye Diri, gwamnan jihar Bayelsa kuma dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, ya yi nasara a akwatin zabensa.
Diri ya yi kayar da manyan abokan hamayyarsa ya yi nasara a akwatin zabe na Sampou/Kalama Ward, PU, 004, Kolokuma/Opkuma LG, Jihar Bayelsa.
Gwamnan, wanda ke neman wa'adi na biyu a zaben tare da wasu yan takara 15, ciki har da, Timipre Sylva na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da takwararsa na Labour Party (LP), Udengs Eradiri, ya samu kuri'u 218.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sylva ya samu kuri'u 0, shi kuma Eradiri ya samu kuri'u 0 shima.
Kuri'un da aka samu a akwatin Diri:
Sampou/Kalaman Ward, PU 004, Kolokuma/Opokuma LG, Bayelsa.
APC - 0
ADP - 1
PDP - 218
LP - 0
Asali: Legit.ng