Zaben Gwamnan Kogi: Yan Daba Sun Kashe Mai Goyon Bayan APC a Anyigba

Zaben Gwamnan Kogi: Yan Daba Sun Kashe Mai Goyon Bayan APC a Anyigba

  • Wasu yan daban siyasa sun farmaki rumfar zabe yayin da ake tsaka da kada kuri'a a yankin Anyigba da ke jihar Kogi
  • Maharan dauke da muggan makamai sun bindige wani mutum mai suna, Umar Hassan
  • An yi zargin cewa maharan sun yi ta yi wa yan APC barazana tare da shan alwashin kashe duk wanda bai zabi SDP ba a zaben gwamnan da ke gudana a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Kogi - Wasu da ake zaton yan daba ne sun bindige wani mai goyon bayan jam'iyyar APC, Umar Hassan mai shekaru 35 a rumfar zabensa ta Agala Ogane, Anyigba.

Tsoro ya kama masu kada kuri'a a rumfar zaben yayin da yan daba suka kai farmaki, inda suka yi barazanar kashe duk wanda ya kada kuri'ar da ya saba "Ajandar Igala".

Kara karanta wannan

Zaben Kogi: Sojoji sun tare hanya, sun hana dan siyasa da tawagar 'yan sandan wuce wa

Yan daba sun halaka wani a zaben Kogi
Zaben Gwamnan Kogi: Yan Daba Sun Kashe Mai Goyon Bayan APC a Anyigba Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

"Yan bindiga sun yi barazanar kashe duk wanda bai zabi SDP ba", Wanda abun ya faru a idonsa

Wani ganau ya fada ma manema labarai cewa yan daban sun farmaki rumfar zaben da muggan makamai, inda suka yi barazanar kashe duk wanda bai zabi jam'iyyar SDP ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Lamarin ya kasance kamar abin da muke kallo a fina-finai masu ban tsoro yayin da suka mamaye rumfar zabenmu dauke da muggan makamai. Abun takaici, abun ya cika da Hassan sannan aka harbe shi.
"Suna ta wakokin yaki cewa za su kashe duk wanda ya yi zabe sabanin Ajandar Igala. Sun yi ta harin Hassan kasancewarsa dan APC.
"Abun da ya fi bani mamaki shine cewa sojojin da suke ta yi wa magoya bayan APC barazana da kamu basa wajen don ceto ran Hassan. Wannan abun takaici ne."

Ana ta zabe cike da kwanciyar hankali a rumfunar zabe da dama a Anyigba har sai da yan bindigar suka farmaki rumfuna da dama don yaki da duk wanda suke zargin dan APC ne.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun kori masu zabe a Bayelsa, sun yi harbe-harbe

APC ta yi martani kan harin

Rahotanni sun nuna cewa zuwa yanzu ana gudanar da zabe cikin lumana a yankin tsakiya da yamma.

Da aka tuntube shi, kakakin kungiyar kamfen din gwamnan APC, Hon. Kingsley Fanwo Yya yi Allah wadai da harin sannan ya bukaci hukumomin tsaro da su zakulo makasan ba tare da bata lokaci ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng