"15k daga APC, PDP na biyan 13k", Ana Zargin Siyan Kuri'a a Bayelsa, Bayanai Sun Fito

"15k daga APC, PDP na biyan 13k", Ana Zargin Siyan Kuri'a a Bayelsa, Bayanai Sun Fito

Ana ta zargin siyan kuri'u a wasu yankuna yayin da ake gudanar da zaben gwamnan jihar Bayelsa inda aka rahoto jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da All Progressives Congress (APC) suna siyan kuri'u.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A wani wallafa na Twitter da The Cable ta yi, an jiyo masu zabe a mazabar PU 07, Ward 10, karamar hukumar Yenagoa suna magana kan zargin siyan kuri'u a garin Ekpetiama.

Ana zargin siyan kuri'a a zaben Bayelsa
Ana zargin jam'iyyun APC da PDP na siyan kuri'u a Bayelsa. Hoto: Photo Credit: Duoye Diri, Timipre Sylva
Asali: Twitter

An rahoto daya daga cikin masu zaben yana cewa APC na biyan naira dubu 15 yayin da PDP ke biyan naira dubu 13.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakon na Twitter:

"An jiyo suna magana kan zargin siyan kuri'u. An jiyo wani mai zabe yana cewa: N15k daga APC, N13K daga PDP."

Kara karanta wannan

Zaben jihohi: Gagarumar matsala yayin da aka fara siyan kuri'u N15k, an bayyana mazabun

A halin yanzu Bayelsa na karkashin jam'iyyar PDP inda Gwamna Duoye Diri, wanda ke neman wa'adi na biyu yana fafatawa da tsohon gwamnan jihar, Timipre Sylva.

Diri ya zama gwamnan jihar shekaru hudu da suka shude a Kotun Koli bayan kotu ta kori David Lyon wanda ya lashe zaben 2019, bayan an same mataimakinsa da laifin kirkirar takardan karatu na bogi.

Gwamnan na PDP yana majalisa a matsayin sanata kafin kotun kolin ta yanke hukuncin soke nasarar Lyon da mataimakinsa yan kwanaki bayan rantsar da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164