Zaben Gwamnan Bayelsa: Jam’iyyar LP Ta Gamu da Gagarumin Matsala

Zaben Gwamnan Bayelsa: Jam’iyyar LP Ta Gamu da Gagarumin Matsala

  • Yayin da aski ya zo gaban goshi, dan takarar jam'iyyar LP a zaben gwamnan jihar Bayelsa, Udengs Eradiri, ya gamu da babban matsala
  • Ciyamomin kananan hukumomi shida cikin takwas da jam'iyyar ke da su sun yi watsi da Eradiri, ana gobe zabe
  • Sun yi zargin cewa ba a sako su a cikin harkokin yakin neman zaben dan takarar nasu ba
  • A yau Asabar, 11 ga watan Nuwamba ne al'ummar jihar Bayelsa ke zaben sabon gwamna da zai shugabance su na shekaru hudu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wasu ciyamomin kananan hukumomi karkashin inuwar LP a jihar Bayelsa sun yi watsi da dan takarar gwamna na jam'iyyarsu, Udengs Eradiri, a ranar jajiberin zaben gwamna a jihar.

Kara karanta wannan

Dakarun soji sun damke wasu motoci 3 da ake zargi a zaben jihar Kogi

Shida daga cikin ciyamomin kananan hukumomin takwas sun ce sun dauki matakin ne saboda tsame su da shugabancin LP ta yi daga tsarin yakin neman zaben gwamnan.

Ciyamomin LP 6 sun sauya sheka a jihar Bayelsa
Zaben Bayelsa: 6 Daga Cikin Ciyamonin LP 8 Sun Fice Daga Jam’iyyar, Sun Fadi Dalili Hoto: Peter Obi
Asali: Facebook

Shugabannin jam'iyyar sun yi zargin cewa Eradiri ya kunyata su a idon duniya, ya yi watsi da su da zaginsu duk da shawarar da suka ba shi kan ya bari su shiga harkokin kamfen din.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun bayyana matakin nasu ne a cikin wata sanarwa da suka fitar a Yenagoa, babban birnin jihar a ranar Juma’a, 10 ga watan Nuwamba, inda suka ce wasikun da suka rubuta na bayyana gaban shugabannin jam’iyyar na jihar da shawarwarin yin aiki tare bai cimma nasara ba.

Ciyamomin sun kuma zargi dan takarar gwamnan da kin rantsar da kwamitin yakin neman zaben amma ya yanke shawarar nada tsarin kamfen na mutum biyu, wadanda yan aike ne kawai a wajensa.

Kara karanta wannan

Zaben 11 ga watan Nuwamba: Jerin gwamnonin jihar Bayelsa daga 1999 zuwa yanzu

Jerin sunayen ciyamomin jam'iyyar da suka raba gari da dan takararsu a zaben gwamnan Bayelsa

Ga jerin sunayen ciyamomin da suka bar jam'iyyar: Super Kworkwor (Yenagoa), Ifiemi Ilahnyog (Southern Ijaw), Clinton Naru Emesua (Ogbia), Tamuno Deifugha (Kolokuma/Opokuma), Warri Moses (Sagbama) da Appi Ebierelayefa Stephen (Nembe).

Ci gaban na zuwa ne a ranar jajiberin zaben gwamna a jihar, wanda aka shirya yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, kamar yadda jadawalin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ya sanar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng