Kotun Daukaka Ƙara Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Ɗan Majalisar Tarayya Bayan Kotu Zaɓe Ta Tsige Shi
- Bayan Kotun zaɓe ta soke nasararsa, ɗan majalisar tarayya na LP daga Legas ya samu nasara a Kotun ɗaukaka ƙara
- Kotun ta jingine hukuncin farko, kana ta tabbatar da Thaddeus Attah a matsayin sahihin ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Eti Osa a Legas
- Kwamitin Kotun ɗaukaka ƙara ya ce shaidun da ƙaramar Kotu ta dogara da su ba su inganta ba
Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Kotun ɗaukaka ƙara ta sake tabbatar da nasarar Mista Thaddeus Attah na Labour Party a matsayin ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Eti Osa a jihar Legas.
A baya Kotun sauraron korafe-ƙorafen zaben ƴan majalisar tarayya da na jiha mai zama a Tafawa Balewa Square, jihar Legas ta rushe nasarar Otta, kamar yadda Premium Times ta tattaro.
Amma a ranar Alhamis, 9 ga watan Nuwamba, 2023, Kotun daukaka ƙara ta jingine hukuncin Kotun zaɓen kana ta maida wa Otta kujerarsa ta ɗan majalisar tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa ta soke hukuncin Kotun zaɓe?
Kwamitin alkalai uku na Kotun ya aminta da bayanan lauyan ɗan majalisar, Mike Ozekhome (SAN) cewa Kotun zaɓen ta yi kuskure a hukuncin da ta yanke.
Kotun ɗaukaka ƙarar ta gamsu cewa ƙaramar Kotun ta yi kuskure yayin da ta dogara da takardun da wasu shaidu, waɗanda ba wakilan jam'iyya ba, suka gabatar mata.
Ta bayyana cewa shaidun sun bayyana ne kawai a gaban kotun don gabatar da Fam EC8A (takardun sakamakon zabe a rumfuna) wanda ba su da alaƙa da shi.
Kotun ta ce bai kamata kotun zaɓe ta dogara da shaidar shaidun ba wajen tantance gaskiyar runfunan da aka gudanar da zabe ko aka soke zabe ba.
Bisa haka ta yanke cewa saɓanin hukuncin ƙaramar Kotu, zaben da aka gudanar a mazaɓar ya kammala, kana ta soke umarnin INEC ta shirya sabon zaɓe ciko cikin kwanaki 90.
Daga nan Kotun ɗaukaka ƙara ta soke hukuncin Kotun zaɓe kana ta tabbatar wa ɗan Majalisar da kujerarsa ta mamba a majalisar wakilan tarayya, The Cable ta ruwaito.
Kotu ta yi hukunci kan zaben jihar Akwa Ibom
A wani labarin na daban Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan ƙarar da jam'iyyu biyu suka kalubalanci nasarar Gwamna Eno na Akwa Ibom
Yayin yanke hukunci ranar Jumu'a, Kotun ta kori ƙarar AA da AP bisa rashin cancanta, ta amince da hukuncin Kotun zaɓe.
Asali: Legit.ng