Zaben Gwamnan Bayelsa Na 2023: Jerin Sunayen Yan Takara 16 da Jam’iyyunsu

Zaben Gwamnan Bayelsa Na 2023: Jerin Sunayen Yan Takara 16 da Jam’iyyunsu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Yenagoa, jihar Bayelsa - A jihar Bayelsa, yan takara da jam'iyyun siyasa 15 ne za su fafata da Gwamna Douye Diri na jam'iyyar PDP a zaben gwamna na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Manyan abokan hamayyar Diri sune tsohon gwamna kuma tsohon karamin ministan man fetur, Timipre Sylva na APC da Udengmobofa Eradiri na LP, da kuma wasu 13. Za su fafata da gwamnan a ranar Asabar don sanin shugaban jihar na gaba.

Yan takara 16 ne za su fafata a zaben gwamnan Bayelsa
Zaben Gwamnan Bayelsa Na 2023: Jerin Sunayen Yan Takara 16 da Jam’iyyunsu Hotoi: Timipre Marlin Sylva, Douye Diri, Udengmobofa Eradiri
Asali: Facebook

INEC ta saki jerin sunayen yan takara a zaben Bayelsa

Kasa da sa'o'i ashirin da hudu kafin zaben, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta tattara jerin sunayen manyan yan takara 16 da ke neman kujerar gwamna da fafatawa da Diri don jagorantar jihar na shekaru hudu masu zuwa.

Kara karanta wannan

Zabukan Kogi, Imo, Bayelsa: Malamin addini ya ce APC za ta lashe jihohi 2, ya bayyana su

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga jerin sunayen da INEC ta saki a kasa:

1. Gwamna: Idikio Warmate Jones (Accord Party)

Mataimakin gwamna: Owo Desmond Inodu

2. Gwamna: Bufumoh Akpoebi Alex (Action Alliance Party)

Mataimakin gwamna: Okoya Ledebi Lilian

3. Gwamna: Kalango Stanley Davies (African Democratic Congress ADC)

Mataimakin gwamna: Obesi Otasome Benjamin

4. Gwamna: Oguara Nengimonyo (ADP)

Mataimakin gwamna: Omonibo Angonimi

5. Gwamna: Sylva Timipre Marlin (All Progressives Congress)

Mataimakin gwamna: Maciver Joshua

6. Gwamna: Subiri Waibodei Joseph (APGA)

Mataimakin gwamna: Lott Kime Thompson

7. Gwamna: Osharikeni Saturday (APM)

Mataimakin gwamna: Ugbenbo Woyindeinyefa

8. Gwamna: Ogege Kemelayefa Mercy (APP)

Mataimakin gwamna: Leigh Robertson Kirk

9. Gwamna: Ben Victor Magbodo (Boot Party BP)

Mataimakin gwamna: Ineinei Ebiowei Major

10. Gwamna: Eradiri Udengmobofa (Labour Party)

Kara karanta wannan

Abin da ya faru bayan an sace daliban Jami'ar Zamfara – Matawalle ya magantu

Mataimakin gwamna: Nathus Benjamin

11. Gwamna: Azebi Bestman Ayabeke (New Nigeria Peoples Party)

Mataimakin gwamna: Ganagana Ebimowei

12. Gwamna: Micah Akeems

Mataimakin gwamna: Ziprebo Pius Emomotimi

13. Gwamna: Diri Douye (PDP)

Mataimakin gwamna: Ewhrudjakpo Oborawharievwo Lawrence

14. Gwamna: Ozato Erepadei Erepadei (PRP)

Mataimakin gwamna: Okala Azibola

15. Gwamna: Osuluku Binalayefa (SDP)

Mataimakin gwamna: Doibo Ebinabo

16. Gwamna: Simeon Imomotimi Karioru (ZLP)

Mataimakin gwamna: Josiah Famvie

An nemi a soke takarar Douye Diri

A wani labarin, mun ji cewa kasa da kwanaki a gudanar da zaɓen gwamnan Bayelsa, an shigar da wata sabuwar ƙara ta neman soke takarar gwamna Douye Diri da mataimakinsa, Lawrence Ewhrudjakpo, a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Ƙarar dai ta nemi umarnin tilasta hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta cire sunayen Diri da Ewhrudjakpo a matsayin ƴan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen ranar 11 ga watan Nuwamba, cewar rahoton Premium Times.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng