Zaben Gwamnan Kogi: Fitaccen Malami Ya Bayyana Wanda Zai Lashe Zabe, Ya Fadi Dalili

Zaben Gwamnan Kogi: Fitaccen Malami Ya Bayyana Wanda Zai Lashe Zabe, Ya Fadi Dalili

  • Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya ce APC za ta yi duk mai yiwuwa don ci gaba da mulki a jihar Kogi, lamarin da ya dakushe muradin Sanata Dino Melaye
  • Da yake martani kan zaben gwamnan jihar Kogi mai zuwa, Primate Ayodele ya ce ya hango rudani a babbar jam'iyyar adawa ta PDP
  • Primate Ayodele ya bayyana cewa za a yi rikici a zaben, inda ya bukaci jami'an tsaro da su shirya ma aikin da ke gaba

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Lokoja, jihar Kogi - Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, ya yi hasashen cewa jam'iyyar APC mai mulki za ta lashe zaben gwamna a jihar Kogi, wanda za a yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Zabukan Kogi, Imo, Bayelsa: Malamin addini ya ce APC za ta lashe jihohi 2, ya bayyana su

Alhaji Ahmed Ododo shine dan takarar jam'iyyar APC, kuma shine dan takarar da gwamna mai ci, Yahaya Bello ke goyon baya.

Primate Elijah Ayodele, ya ce APC ce za ta lashe zaben gwamnan Kogi
Zaben Gwamnan Kogi: Fitaccen Malami Ya Bayyana Wanda Zai Lashe Zabe, Ya Fadi Dalili Hoto: @KogiLiberation, @_dinomelaye, @scarfizal
Asali: Twitter

"APC ce za ta yi nasara a zaben Kogi" - Ayodele

Da yake hasashe gabannin zaben, Primate Ayodele ya ce jam'iyyun SDP, PDP da sauransu za su sha kaye a kokarinsu na yin waje da APC. Malamin addinin ya yi nuni ga hadin kan jam'iyyun adawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya rubuta a shafinsa na dandalin X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) cewa:

"A jihar Kogi, jam'iyya mai mulki ce za ta yi nasara a zaben gwamna mai zuwa. Yan adawa sun gaza yin maja don kayar da APC.
"Hadewar yan adawa ne kadai zai iya ba su nasara a kan APC."

Malami ya yi hasashen zabukan jihohi 3

A wani labari makamancin wannan, Apostle Ako Anthony na cocin Mountain of Christ Prayer Ministry International ya yi hasashen cewa jam'iyyar APC za ta lashe jihohi biyu a zaben da za a yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Zaben Kogi: Yadda za ta kaya tsakanin APC, PDP da SDP, an yi hasashen mai nasara

A yayin wani shirin kai tsaye a dandalin Facebook a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba, wanda jaridar Legit ta gani, Apostle Anthony ya ce babbar jam'iyyar adawa ta PDP za ta lashe zabe a jihar Bayelsa. Gwamna Duoye Diri ne dan takarar PDP a jihar Bayelsa.

A cewar Apostle Anthony, a jihar Imo, Hope Uzodimma zai kwato kujerarsa ta kowani hali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng