“Na Hango Zubar Jini”: Malamin Addini Ya Yi Hasashe Mai Ban Tsoro Game da Zaben Gwamnan Kogi
- Fasto Eneojo Suleman ya yi gargadi kan yiwuwar barkewar rikici a zaben gwamna mai zuwa a jihar Kogi
- Fasto Suleman ya yi hasashe kan yadda sakamakon zaben za ta kasance, yana mai cewa APC ce da nasara
- Malamin addinin ya kuma yi hasashe mai kyau game da jam'iyyar SDP da dan takararta Murtala Ajaka
Jihar Kogi - Eneojo Suleman, babban fasto a cocin Hill of Shalom Global Ministry, ya bayyana cewa zaben gwamna da za a yi a jihar Kogi "zai kasance mai zafi".
Fasto Sulam ya ce ya hango kazamin karo a yayin zaben.
Kogi: "Tsakanin Muri da APC ne wani zai lashe zaben"
Malamin addinin ya kuma yi hasashen cewa tsakanin Murtala Ajaka (Muri) na jam'iyyar SDP da dan takarar jam'iyyar APC mai mulki, Ahmed Ododo, ne wani zai lashe zaben da za a yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba. Fasto Suleman ya kasance haifaffen dan jihar Kogi ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya rubuta a shafinsa na Facebook:
"Hasashe kan zaben Kogi!
"Zaben Kogi zai kasance mai zafi. Na gano rikici da caccaka mutuwa, da jini.
"Wanda zai ci zabe tsakanin Muri da APC ne.
"Mutanen Muri sun yi zabi amma ban san dalilin da yasa nake ganin APC a mulki ba."
Ya ci gaba da cewa:
"Mu taya Kogi da addu'a. A karshe, na hango shari'a ta biyo bayan zaben.
"Addu'a ta na tare da Kogi don samun zaman lafiya da dan takarar da ya dace a Kogi."
Malamin addini ya yi hasashe kan zaben Kogi
A wani labarin kuma, mun ji cewa ma'assasin majami'ar Jehova's Eye Salvation, manzo Godwin Ikuru, ya ce babu ta yadda za a yi dan takarar jam'iyyar SDP, Murtala Ajaka, ya lashe zaben gwamnan jihar Kogi a zaben jihar mai zuwa.
Manzo Ikuru ya ce duk da Ajaka shi ne ya mafi shahara a cikin 'yan takarar, sai dai a cewar sa, "ba shi da taimakon na-sama". Malamin majami'ar ya yi hasashen cewa Ajaka zai yi makoma irin ta Peter Obi.
Jaridar Legit Hausa ta ruwaito maku cewa Obi shi ne na uku a zaben shugaban kasa da ya gabata, wanda ya samu goyon bayan jama'a a zaben da aka gudanar cikin watan Fabreru.
Asali: Legit.ng