Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Sanata Kawu Sumaila da Dan Majalisar NNPP

Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Sanata Kawu Sumaila da Dan Majalisar NNPP

  • Kotun daukaka kara ta yanke hukunci a kan karar zaben sanatan Kano ta Kudu da na dan an majalisar tarayya mai wakiltar Gaya/Ajingi/Albasu
  • A ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba, kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar zaben Abdulrahman Kawu Sumaila a matsayin sanatan Kano ta Kudu
  • Haka kuma, kotun ta tabbatar da nasarar Hon Dr. Ghali Mustapha Tijjani na NNPP a matsayin dan majalisar tarayya mai wakiltar Gaya/Ajingi/Albasu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Kano - Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar da ake a kujerar sanatan Kano ta kudu da kuma na mazabar Tarayya ta Gaya/Ajingi/Albasu a jihar Kano.

Kotun wacce ta yanke hukunci a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba, ta tabbatar da nasarar Abdulrahman Kawu Sumaila na jam'iyyar NNPP, a matsayin sanatan Kano ta kudu.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta gama aiki, ta yanke hukunci kan nasarar dan majalisar tarayya na PDP

Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar zaben yan NNPP 2 a Kano
Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Sanata Kawu Sumaila da Dan Majalisar NNPP Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Haka kuma, kotun daukaka karar, ta kuma tabbatar da Hon Dr. Ghali Mustapha Tijjani na NNPP a kan kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar Gaya/Ajingi/Albasu.

Hadimin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso a bangaren yada labarai, Saifullahi Hassan ne ya bayyana haka a shafinsa na X wanda aka fi sani da Twitter.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Ghali Mustapha ya yi martani a kan nasarar da ya samu a kotu

Har ila yau, dan majalisar tarayya mai wakiltar Gaya/Ajingi/Albasu ya tabbatar da nasarar da ya samu a kotun daukaka karar a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook.

Ghali Mustapha ya rubuta a shafin nasa:

Alhamdulillah kotun daukaka kara ta tabbatar da zabena a yau.

Jama'a sun yi martani a wallafar Hon. Ghali Mustapha

Muhammad Mustapha Utai ya yi martani:

Kara karanta wannan

Kano: Kotun daukaka kara ta sake yanke hukunci kan zaben Majalisar Tarayya, ta yi bayani

"Allah ya Karo daraja da girma."

Al-awwal Yusuf ya yi martani:

"Masha Allah na tayaka murna yallabai Allah madaukakin sarki ya yi maka jagora a duk inda kake Alhamdulillah."

Ismail Abubakar Ajingi ya ce:

"Masha Allah na tayaka murna yallabai."

Auwalu Ajingin ya ce:

"Allah yasa hakace Tafi Alkhairi A Garemu Da Jam'yyarmu Da Dantakararmu Hon Abdullahi Mahmud Gaya, Kaikuma Allah ya Baka Ikon Yiwa Gaya Ajingi Da Albasu Aiyukan Alkhairi Da Kyautatawa Yaki ya Kare Zamu Tara 2027."

Dan majalisa na PDP ya tabbata a kujerarsa

A wani labarin kuma, mun ji cewa bayan doguwar shari'a da aka dade ana yi, kotun daukaka kara, reshen lagas, ta tabbatar da zaben Hon. Ikenga Imo Ugochinyere Ikeagwuonu, dan majalisa mai wakiltan mazabar Ideato ta arewa da kudu ta jihar Imo a majalisar wakilai.

Da take yanke hukunci a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba, kotun ta ayyana Hon. Ikenga Ugochinyere a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben dan majalisar wakilai a jihar Imo a zaben na watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng