"Kotun Ƙoli Ba Ta Tabbatar da Nasarar Tinubu a Zaben 2023 Ba" Datti Ya Faɗi Abu 1 da Kotun Ta Yi
- Ranar Litinin 6 ga watan Nuwamba, Peter Obi ya gudanar da taron manema labarai kan hukuncin Kotun ƙoli da ya tabbatar da nasarar Tinubu
- Yayin da Obi ya jaddada cewa yanzu aka fara, abokin takararsa, Datti Baba-Ahmed ya kafe kan cewa ba Tinubu ne ya ci zaɓen 2023 ba
- Obi da Datti sun caccaki Kotun kolin Najeriya da zargin cewa ta sauka daga tsarin da aka kafa Kotunan doka
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a inuwar LP a zaɓen 2023, Dakta Yusuf Datti Baba Ahmed, ya yi martani kan hukuncin Kotun kolin Najeriya.
Datti Baba-Ahmed ya ce Kotun ƙolin Najeriya ba ta ayyana shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ba.
Abokin takarar Obi ya kafe Tinubu bai ci zaɓe ba
Ya yi wannan furucin ne a wurin taron manema labaran da suka gudanar ranar Itinin, 6 ga watan Nuwaba, 2023 kan hukuncin da Kotun Allah ya isa ta yanke, The Sun ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwa LP da Datti Baba-Ahmed sun yi wannan taro ne mako biyu bayan shugaba Tinubu ya samu nasara a Kotun ƙoli.
Da yake nasa jawabin, abokin takarar Obi watau Datti, ya jaddada cewa Kotu ba ta tabbatar da nasarar Tinubu ba amma ta goyi bayan ƙetare dokar da Kotun zaɓe ta yi.
A cewarsa, Kotun daga ke sai Allah ya isa ta amince da take dokar da Kotun sauraron kararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta yi, amma ba ta tabbatar da nasarar Tinubu ba.
Datti ya ce mutumin da ya yi jabun satifiket dinsa kuma yake da kashin kaji a safarar miyagun ƙwayoyi ba zai taɓa girgiza shi ba.
A kalamansa, ya ce:
"Kotun koli ba ta tabbatar da shugabancin Bola Ahmed Tinubu, ta dai tabbatar da take dokar ƙaramar Kotu."
INEC ta bi umarnin Kotun ɗaukaka ƙara
A wani rahoton na daban Hukumar zabe ta ƙasa INEC ta yi gyara a jerin sunayen ƴan takarar da zasu fafata a zaben gwamnan jihar Bayelsa.
A sabon jerin sunayen da INEC ta buga a shafinta, ta ƙara sunan ɗan takarar APC, Timipre Sylva da mataimakinsa, Maciver Joshua.
Asali: Legit.ng