Nasarar Tinubu: Peter Obi Ya Yanke Shawara Kan Sake Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa a 2027
- Mista Peter Obi ya ce tafiyar siyasar da ya ɗauko ta neman shugabancin Najeriya yanzu aka fara, ba zai haƙura haka nan ba
- Tsohon gwamnan ya nuna alamun cewa zai sake gwabza neman ɗarewa kujera lamba ɗaya a zaben shugaban ƙasa na 2027
- Ya kuma yaba wa sadaukarwan matasan Obidient, inda ya ce karsashin da suka nuna a lokacin zaɓe ba ƙaramin abin mamaki bane
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar Labour Party a zaben 2023 ya bayyana alamar da ke nuna cewa zai sake neman takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya.
Mista Obi, tsohon Gwamnan jihar Anambra ya ayyana cewa yanzu ya fara tafiyar siyasa, alamar da ke nuna burinsa na kwace mulki hannun Bola Tinubu a zaɓen 2027.
"Kotun ƙoli ba ta tabbatar da nasarar Bola Tinubu a zaɓen 2023 ba" Datti ya faɗi abu 1 da kotun ta yi
Ya faɗi haka ne a wurin taron manema labarai wanda ya gudanar ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, 2023 kan hukuncin da Kotun ƙoli ta yanke, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan baku manta ba Kotun daga ke sai Allah ya isa ta tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaben 25 ga watan Fabrairu, yayin zaman yanke hukunci ranar 26 ga watan Oktoba.
Shin Peter Obi zai jingine siyasa?
Da yake jawabi a wurin taron ƴan jaridan, Mista Obi ya ce tafiyar siyasar da ya ɗauko a matakin ƙasa yanzu aka fara ma'ana zai sake neman takara a zaɓe na gaba.
Ya kuma miƙa godiya ga ɗaukacin ƴan Najeriya musamman matasa waɗan da suka sadaukar da kansu, suka tsaya tsayin daka, suka mara masa baya.
Jaridar Vanguard ta tattaro Obi ma cewa:
"Ƴan Najeriya sun mara mana baya ba don komai ba sai don kishin ƙasa da kuma muradin su na ganin ƙasar ta samu jagorori na gari masu hangen nesan da zasu shugabanci Najeriya zuwa tudun mun tsira."
"Karfi, kuzari da sadaukarwan da matasan Najeriya da ƴan tafiyar Obidient suka nuna abun ban mamaki ne, na yaba musu kuma na sara masu."
"Ina tabbatar masu da cewa wannan ba shi ne ƙarshen tafiyar da muka ɗauko ba, amma a taƙaice wannan ne mafari, yanzu aka fara."
- Peter Obi.
Jiga-jigan PDP sun koma APC
A wani rahoton kuma Tsohon ministan ayyuka da tsohon ɗan takarar gwamna sun fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC a jihar Edo.
Jiga-jigan biyu, Arch Mike Onolememen da Gideon Ikhine tare da magoya bayansu sun samu tarba mai kyau ranar Litinin.
Asali: Legit.ng