Sanata Ya Jagoranci Yan PDP Fiye da 2000 Sun Koma APC Bayan Hukuncin Kotun Koli

Sanata Ya Jagoranci Yan PDP Fiye da 2000 Sun Koma APC Bayan Hukuncin Kotun Koli

  • Sanata Akinyulure ya jagoranci magoya bayansa sun fice daga PDP zuwa APC a Ondo
  • Shugaban jam'iyyar APC a Ondo, Adetimehin ya ce wannan nasara ce babba kasancewar zaben gwamna na daf a jihar
  • Ademehin ya ce kyakkyawan shugabancin gwamnatin Akeredolu ce sirrin nasarar APC a Jihar Ondo ya na mai cewa za su kuma lashe zaben 2024 mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Jihar Ondo - Sama da yan PDP 2000 ne suka sauya sheka jam'iyyar APC mai mulki a Idanre, da ke karamar hukumar Idanre a Jihar Ondo.

Sun sauya shekar ne karkashin jagorancin Sanata Ayo Akinyulure, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Yan PDP fiye da 2000 sun koma APC a Ondo
Sanata Akinyulure ya jagoranci mambobin PDP fiye da 2000 sun koma APC bayan hukuncin kotun koli: Hoto: Photo credits: @ayo_akinyelure, @IdanreTv
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Jami'an NDLEA sun kame tan 6 na ganyen maye a jihohin Najeriya shida 5, bayanai sun fito

Abin da yasa na koma APC, Sanata Akinyulere

Sanata Akinyulure ya ce ya koma APC ne saboda ya yadda da martabar Najeriya a hannun gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Akinyulure ya ce:

"Na ji dadi na dawo gida. Tushe na nan kuma na baro PDP don kara wa APC kima.
"Akalar yan Jihar Ondo, kamar yadda zaben da ya gabata ya nuna gaba daya ana goyon bayan Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa bayan ya lashe gaba daya kananan hukumomi 18 na jihar karo na farko a tarihi. Wannan ya nuna tabbas yan Ondo na goyon bayan manufofin shugaba Tinubu.
"Saboda haka, yau na ke sanar da komawa APC a hukumance don taimaka wa gwamnatin Asiwaju, wanda ubangidana ne, kuma jagoran da nake koyi da shi tun da na fara siyasata a Lagos, karamar hukumar Alimosho kuma a matsayin shugaban LARIP lokacin da Tinubu ke matsayin gwamnan Lagos."

Kara karanta wannan

Bode George Yana Shirin Barin Najeriya Bayan Kotun Koli Ta Tabbatar da Nasarar Tinubu? Jigon PDP Ya Magantu

Ya cigaba da cewa:

"A matsayi na na dan siyasa da aka sani da taimakon al'umma, dole na nemi in da aka damu da damuwar al'umma kamar dai APC a mulkin Tinubu.
"Saboda haka ni da duk magoya baya na da masu ruwa da tsaki na Ondo ta tsakiya da Jihar Ondo gaba daya musamman karamar hukumar Idanre muka ga dacewar a samu shugabanci mai kyau a Ondo, a farfado da siyasar jihar don daga martabar jihar da mutanen ciki karkashin jagorancin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu."

APC za ta cigaba da mulkar Najeriya da Ondo, Ademehin

Shugaban jam'iyyar APC a Jihar Ondo, Ade Ademehin, wanda ya karbi masu sauya shekar ya ce jam'iyyar zata cigaba da mulki a jihar da kasa gaba daya.

Adetimehin ya ce APC ce za ta lashe zaben gwamna da za a gudanar a jihar a shekara mai kamawa saboda manyan yan siyasa sun ajiye kowacce jam'iyya sun rungumi APC.

Kara karanta wannan

'Yan Siyasa 5 Masu Neman Shugaban Kasa da Tinubu Ya Bai Wa Mukami a Gwamnatinsa

Ya ce nasarar da jam'iyyar ke samu na da alaka da irin ayyukan alherin da gwamnatin Akeredolu ta yi a jihar.

Adetimehin ya ce:

"Zaben gwamna mai kamawa ba batun sulhu, muna da kyakkyawan yakini da ke karuwa a kowace rana saboda yadda aka kurbi romon dimukradiyya a Ondo ba tare da rikici ba.
"Ina mai tabbatar mu ku nan da yan watanni, PDP zata fada makoki, duba da yadda shugabanninta ke fita suna dawowa jam'iyyar APC."

Kaduna: Kansilolin jam'iyyar PDP 19 sun koma APC

A wani rahoton, kimanin kansiloli 19 na jam'iyyar PDP ne suka sauya sheka zuwa APC tare da magoya bayansu a jihar Kaduna.

Kansilolin sun bayyana cewa jagoranci nagari da ma'ana karkashin gwamnan jihar ne yasa suka fice daga PDP suka koma APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164