Jam'iyyar APC Ta Dakatar Kamfe Sakamakon Hatsarin Jirgin Ruwa a Bayelsa
- Hatsarin jirgin ruwa ya sa jam'iyyar APC ta dakatar da gangamin yaƙin neman zaɓen ɗan takararta a jihar Bayelsa
- Shugaban APC na jihar, Dennis Otiotio, ya ce haɗarin ya rutsa harda mambobin tawagar kamfen wanda ba a ceto ba har yanzu
- Ya ce sun sanar da hukumomin da ya kamata kuma tuni aka fara kokarin lalubo babban jigon da ya nutse
Jihar Bayelsa - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta dakatar da yaƙin neman zaɓen ɗan takararta na gwamna a jihar Bayelsa sakamakon haɗarin jirgin ruwa.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro, jam'iyyar APC ta ɗauki wannan matakin saboda hatsarin jirgin ruwan ya rutsa da wasu mambobin kwamitin kamfe.
Lamarin ya faru ne a lokacin da tawagar yakin neman zaben jam’iyyar ke dawowa daga karamar hukumar Ogbia bayan kammala gangamin kamfe.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, shugaban APC reshen Bayelsa, Dokta Dennis Otiotio, ya ce jam'iyyar ta sanar da hukumomin da ya dace domin tsamo waɗan da suka nutse a ruwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani sashin sanarwa ya ce:
"Ƙwamitin yaƙin neman zaɓen gwamna na jam'iyyar APC na sanar da al'umma cewa ya ɗage gangamin kamfen da ya tsara yi ranar 26 ga watan Oktoba, 2023 a Nembe-Ogbolomabiri da Nembe-Bassambiri."
"Hakan ta faru ne sakamakon haɗarin jirgin ruwan da ya afku a lokacin kamfen da muka yi yau. A halin da ake ciki ba a ga ɗaya daga cikin ƙusoshin mambobin mu ba."
"Mun sanar da hukumomin da ya dace kuma masu aikin ceto sun yi nisa a ƙoƙarin lalube, zamu tafi hutun kwana ɗaya domin gano bakin zaren kafin ci gaɓa da kamfe ranar Jumu'a.
Za a ci gaba da kamfe ranar Jumu'a
Ya ce harkokin kamfe zasu ci gaba daga ranar Jumu'a a Nembe Ogbolomabiri da Nembe Bassambiri kafin daga bisani ya wuce ƙaramar hukumar Brass ranar Asabar da Lahadi, The Sun ta ruwaito.
Gwamnan APC Ya Gana da Babban Hafsan Tsaro
A wani rahoton na daban Malam Dikko Radda ya jaddada cewa gwamnatinsa ba zata tattauna da 'yan bindiga da sunan tana neman sulhu ba.
Gwamnan ya ce zai yi amfani da isasshen ƙarfin soji wajen magance matsalar tsaro har sai yan ta'adda sun kawo kansu teburin sulhu.
Asali: Legit.ng