Jam'iyyar PDP Ta Dakatar da Shugaban Matasan Jam'iyyar Na Jihar Ondo

Jam'iyyar PDP Ta Dakatar da Shugaban Matasan Jam'iyyar Na Jihar Ondo

  • Jam'iyyar PDP ta dakatar da shugaban matasanta na jihar Ondo jim kaɗan bayan rashin nasarar Atiku Abubakar a Kotun ƙoli
  • A wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, PDP reshen jihar ta umarci ya bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa domin a bincike shi
  • Ta ɗauki wannan matakin ne bisa zarginsa da hannu a aikata wasu ayyuka da ka iya kawo jam'iyyar naƙasu da koma baya

Jihar Ondo - Jam’iyyar Peoples Democratic Party watau PDP reshen jihar Ondo ta dakatar da shugaban matasanta na jihar, Mista Folorunso Makinde.

Mai magana da yawun jam'iyyar PDP na jihar, Mista Kennedy Peretei, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ranar Alhamis.

Babbar jam'iyar adawa ta dakatar da shugaban matasanta na Ondo.
Jam'iyyar PDP Ta Dakatar da Shugaban Matasan Jam'iyyar Na Jihar Ondo Hoto: OfficialPDP
Asali: UGC

Ya bayyana cewa wannan matakin da aka ɗauka ya yi daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin PDP na 2017 wanda aka yi wa garambawul, kamar yadda Punch ta tattaro.

Kara karanta wannan

"Abun Takaici"Jam'iyyar PDP Ta Maida Zazzafan Martani Kan Rashin Nasarar Atiku a Kotun Ƙoli

Sanarwan ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Bisa la'akari ta tanadin sashi na 58(1)(b)(f) da (i) da ke ƙunshe a kundin tsarin mulkin PDP 2017 wanda aka gyara, kwamitin gudanarwa na jiha ya amince da dakatar da shugaban matasa, Folorunso Makinde.
"An dakatar da shi har sai baba ta gani bisa hannu a aikata wasu ayyuka da ka iya ƙara rage ƙima da mutuncin jam'iyyar PDP."
"Bayan haka ana umartan shi da ya bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa nan da kwanaki bakwai masu zuwa domin ci gaba da bincike kan zargin da ake masa."

Yadda siyasa ta ɗau zafi a Ondo

Wannan mataki na zuwa ne yayin da siyasar jihar Ondo ta yi zafi kan rashin ganin gwamna Rotimi Akeredolu, na halartar ofishinsa na gidan gwamnati.

Tun bayan dawowa daga jinya, Gwamnan ya koma zama a gidansa na Ibadan, babban birnin jihar Oyo, lamarin da ya sa matasan PDP suka shirya zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ya Magantu Kan Hukuncin Kotu Ƙoli, Ya Aike da Sako Ga Atiku da Obi

Shirin zanga-zangar matasan ta sa jami'an tsaro suka kwace babbar Sakatariyar PDP da ke Akure, kuma ana hasashen matakin na da alaƙa da dakatar da Mista Makinde, Daily Post ta ruwaito.

Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani

A wani rahoton kuma Babbar jam'iyyar adawa PDP ta nuna tsananin takaicinta bisa kayen da ta sake sha a Kotun ƙolin Najeriya.

Kotun da ake wa taken daga ita sai Allah ya isa ta tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasan 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262