Akpabio Ya Sanya Labule da Shugaba Tinubu Bayan Ndume Ya Fice Daga Zauren Majalisa

Akpabio Ya Sanya Labule da Shugaba Tinubu Bayan Ndume Ya Fice Daga Zauren Majalisa

  • Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ziyarci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba 18 ga watan Oktoba
  • Bayan ganawa da Tinubu, Akpabio ya ce akwai haɗin kai da fahimtar juna a tsakanin sanatocin da ke majalisar
  • Ya yi watsi da iƙirarin cewa akwai rikici a majalisar dattawan Najeriya, inda ya bayyana cewa ƴan majalisar a shirye suke wajen kare muradun ƙasar nan

Aso Rock, Abuja – Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya yi ganawar sirri da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock Villa a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba.

Ganawar ta faru ne kwana ɗaya bayan da babban mai tsawatarwa na majalisar, sanata Ali Ndume, ya fice daga zauren majalisar ana cikin zaman majalisa, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Sabon Shugaban EFCC da Wasu 2 da Tinubu Ya Naɗa, Bayanai Sun Fito

Akpabio ya sanya labule da Tinubu
Akpabio ya sanya labule da Shugaba Tinubu a Villa Hoto: Godswill Akapbio/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Akpabio ya musanta akwai rikici a majalisar dattawa

Akpabio ya shaidawa manema labarai bayan kammala ganawa da shugaban ƙasar cewa akwai hadin kai da fahimtar juna a tsakanin sanatocin yayin da aka ɗan samu rashin jituwa a majalisar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"A majalisa, wani lokacin akan samu saɓani kan batutuwa. Amma ba za mu taɓa kai ga jefa kujeru ba. Majalisar dattawa tana da dattaku, cike take da mutane masu dattako."

Shugaban majalisar ya yi watsi da cewa akwai rikici a majalisar, inda ya ƙara da cewa idan aka samu rashin jituwa, ana gaggawar magance ta idan suka shiga zaman sirri.

"Dukkanmu muna aiki ne bisa manufa daya. Babu matsala ko kaɗan. Ko da wasu mutane ba su yarda da wasu abubuwan da ke faruwa a majalisar dattawa ba, hukuncin mafi rinjaye ne kawai ke yin nasara.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Jihar APC Ta Yi Magana Kan Batun Sake Fitar da Gwamna Mara Lafiya Kasar Waje Domin Jinya

Akpabio ya cigaba da bayyana cewa akwai haɗin kai a cikin majalisar domin sun himmatu wajen cimma muradun ƙasa.

"Mu ƴan siyasa ne, ba ƙiyayya ta dindindin ba sai dai buƙata ta dindindin. Wannan buƙatar ita ce cimma muradun ƙasa." A cewarsa.

Majalisar Dattawa Ta Yi Sauye-Sauye

A wani labarin kuma, majalisar dattawa ta yi sauye-sauye a muƙaman shugabannin da ke jagorantar ta.

Majalisar ta naɗa Sanata Oyelola Yisa Ashiru a matsayin sabon mataimakin shugaban masu rinjaye da a Sanata Nwebonyi Peter Onyeka a matsayin mataimakin mai tsawatarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng